Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mata 19 wadanda aka kama su da laifin shaye-shayen kayan maye a kwaryar birnin Dabo.
Kwamandan Hukumar, Dokta Haruna Ibn-Sina ne ya tabbatar da kame matan kamar yadda wata takarda da jami’in yada labarai na hukumar, Malam Lawal Ibrahim ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
- Majalisar Zartarwa ta amince da kudirin tsawaita shekarun ritayar malamai
- Auren Mata dubu: An daure malami shekara dubu a Turkiyya
Sanarwar ta ce an cafke matan ne suna tsaka da shan kayan maye da misalin karfe 9 na daren ranar Talata 19, ga watan Janairun 2021 a wasu wurin shakatawa biyu da ke kan titin Ahmadu Bello a Unguwar Nasarawa ta jihar.
Ya ce an cafke matan ne yayin da Jami’an hukumaar ke gudanar da sintiri kan masu karya dokar rufe wuraren tarukan biki da gidajen kallo da gwamnati ta bayar da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19 a tsakanin jama’a.
“Dukkan matan 19 da aka kama basu wuce shekaru 20 ba, 18 daga cikin ’yan matan wannan ne karon su na farko, amma dayar an sha kamata da laifin,” in ji shi.
Kwamandan na Hisbah, ya ba wa iyaye shawara da su guji siya wa yaransu manyan wayoyi, kuma su yi kokarin basu tarbiyyar da za ta inganta rayuwarsu su zama mutane nagari.