Dan takarar gwamnan Jihar Kano a jam’iyar Action Democratic Party (ADP) Malam Sha’aban Sharada (OON) ya taya dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyar NNPP, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 66.
Sha’aban wanda dan Majalisar Wakilai ne ya mika sakon taya murnar ne ta hannun hadiminsa, Umar Ibrahim a wata sanarwa da ya fitar a ranar a Litinin.
- Ina makomar Sha’aban Ibrahim Sharada a Siyasar Kano?
- Idan aka sake zaben gwamna a Kano APC za ta fadi —Sha’aban Sharada
Sanarwar ta bayyana cewa, “Abubuwan alheri da tsohon Gwamna Kwankwaso ya assasa a shekarun 1999 zuwa 2003, da kuma shekarun 2011 zuwa 2015 na mulkinsa, ba za a manta da su ba, domin masu gina rayuwar dan Adam ne,” in ji shi.
Sannan ya ce, tsarin Kwankwaso na daukar dauyin karatun dalibai zuwa kasashen turai daya ne daga cikin kyawawan manufofinin da ya kwaikwaya, gami da wasu tsarin gina dan Adam na Malam Ibrahim Shekarau.
Don hake ne a matsayin sa dan Majalisar Tarayya ya tallafa wa matasa mata da maza kimanin dubu dari da sana’o’i daban-daban domin dogaro da kai.
Aminiya ta ruwaito cewa dan takarar gwamnan ya kai yara marasa galihu kimanin 100 kasar waje don yin karatu a fannoni daban-daban karkashin Gidauniyarsa ta Sha’aban Ibrahim Sharada Foundation.
Dan takarar ya kuma yi alkawarin kara farfado da harkar ilimin makarantun gaba da sakantare na gida da isassun ma’aikata da kuma kayan aiki na koyo da koyarwa idan ya samu nasara a Zaben 2023.