Kungiyar Chelsea ta fara shirin neman maye gurbin Kocinta, Frank Lampard, duba yadda kungiyar ke rashin kwazo a wasannin baya-bayan nan da fafata musamman a gasar Firimiyar Ingila, idan aka tunkudo ta tun daga mataki na uku a teburin zuwa mataki na tara.
Jaridar Independent ta ruwaito cewa akwai yiwuwar kungiyar za ta maye gurbin Frank Lampard da daya daga cikin wasu gogaggun masu horaswa da suka hada da Thomas, Tuchel, Max Allegri, Brendan Rodgers da Ralph Hasenhutti.
Ana kuma ganin cewa tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea, Andriy Shevchenko wanda yanzu shi ne kocin tawagar kasarsa ta Ukraine, zai iya maye gurbin Lampard a Stamford Bridge. (Le10 Sport)
Manchester City ta fara sanya idanun lura a kan kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos mai shekara 34, domin sayensa a karshen kakar wasanni ta bana a yayin da kwantaraginsa zai kare da kungiyarsa. (ESPN)
Hakan ya sa gidan talabijin na El Chiringuito ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa da yiwuwar Ramos zai hadu da Lionel Messi a kungiyar PSG a yayin da ta nuna sha’awar fara tattaunawa da zakakurin dan wasan saboda kwantaraginsa da kare a karshen kakar bana.
Kasancewar kwantaraginsa da ya kare a yanzu, Lionel Messi yana cikin makamacin wannan yanayi a Barcelona, a yayin da PSG take son Ramos ya bi sahun dan wasan da ya lashe kyautar Balon d’Or shida.
Arsenal ta yi wa Juventus tayin dan wasanta na tsakiya mai shekaru 32, Mesut Ozil, sai dai Juventus ta fi maida hankali kan matashin dan wasa Dejan Kulusevski mai shekaru 20 wanda ta ke ganin za ta fi cin moriyarsa duba da karancin shekarunsa. (CBS Sport)
An bayar da rahoton cewa Kevin De Bruyne ya yi watsi da tayin farko na kwantaragin Manchester City kuma yana ci gaba da damuwa kan rashin samun wata madogara a tattaunawar da ya ke yi da kungiyar kan wani sabon kwantaragi na tsawon shekaru biyar.
Shekaru biyu da rabi ne suka rage a kwantaragin De Bruyne na yanzu, sai Manchester City ta bude sabuwar tattaunawa da shi a shekarar ta gabata, inda ta nuna sha’awar tsawaita zamansa a kungiyar na wani lokaci mai dogon zango.
Sai dai har yanzu ba a cimma wata matsaya ba a yarjejeniyar kamar yadda The Times ta ruwaito, De Bruyne ya nuna fushinsa a kan tayin farko na kwantaragin da Manchester City ta gabatar masa wanda alamu ke nuna zai yi watsi da shi.
An samu cikas a yarjejeniyar albashi a tattaunawar da kungiyar Real Madrid ke yi kan zawarcin dan wasan Bayern Munich na kasar Austria, David Alaba, a cewar Goal.
Sai dai har yanzu ana sa ran Real Madrid za ta dauki dan wasan, a yayin da har yanzu ta sha gaban Manchester United da Barcelona wajen neman dan wasan.
Tottenham ba ta niyyar sayarwa ko bayar da aron Dele Alli a yayin da kasuwar musayar ’yan wasa ke ci gaba da ci a watan Janairu, kuma tana sa ran dan wasan na tsakiya zai ci gaba da gwagwarmaya domin samun shiga a kungiyar, inji Sky Sports.
Dele Alli ya buga wa Spurs wasanni hudu ne kacal a gasar Firimiyar Ingila ta bana, inda ya zira kwallaye biyu kacal a koma cikin dukkanin wasannin da ya buga a bana.