✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SERAP ta yi ƙarar Tinubu a kotu kan alawus ɗin wasu ministoci

Naɗin waɗanda ke karbar fansho na rayuwa a matsayin ministoci wani aiki ne na son rai.

Ƙungiyar kare haƙƙin ƴan ƙasa da tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya ‘SERAP’ ta kai ƙarar shugaba Bola Tinubu kotu kan gazawar sa wajen hana tsofaffin gwamnonin da suke rike da mukamin minista karbar kudaden fansho na jihohi.

Kungiyar SERAP dai na neman kotu ta tilasta wa Tinubu ya umarci wadannan tsofaffin gwamnonin da su daina karbar irin wadannan kudade.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Lahadi, mataimakin shugaban ƙungiyar a Najeriya, Kolawole Oluwadare, ya ce ministocin da abin ya shafa su ne Nyesom Wike da Bello Matawalle da Adegboyega Oyetola.

Sauran tsofaffin gwamnonin sun hada da Badaru Abubakar da David Umahi da Simon Lalong da Atiku Bagudu da kuma Ibrahim Geidam.

Sanarwar ta ce “Nadin waɗanda ke karbar fansho na rayuwa a matsayin ministoci wani aiki ne na son rai da kuma saɓa wa ƙa’ida.”

“Yayin da da yawa daga cikin ‘yan waɗanda suka ajiye aiki ba a biyan su kuɗaɗen fansho ba, tsofaffin gwamnonin da ke rike da mukamin minista na samun makudan kuɗaɗen alawus-alawus idan sun bar ofis.”

“Gwamnatin Tinubu tana da nauyin hana tsofaffin gwamnonin karbar duk wani hakki na ritaya yayin da suke aiki a matsayin ministoci.”

SERAP dai ta ce wannan dabi’a ba ta dace ba, musamman idan aka yi la’akari da kalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.

Sai dai kuma har yanzu ba a sanya ranar fara sauraron karar ba.