Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50.
NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25.
- Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya?
- Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey
Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya.
SERAP, ta ce wannan karin an yi sa ba bisa ka’ida ba, kuma ya saba wa doka tare da keta hakkin ’yan Najeriya na ’yancin yin magana da samun bayanai.
A cikin karar da ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, SERAP ta nemi kotu ta dakatar da aiwatar da karin kudin, inda ta ce bai halatta ba.
Kungiyar ta yi zargin cewa NCC ba ta bi ka’ida ba kuma ba ta yi la’akari da tasirin da karin zai yi a rayuwar ’yan Najeriya, wadanda da dama ke fama da tsadar rayuwa.
SERAP, ta jaddada muhimmancin samun sadarwa cikin yanayin mai sauki, inda ta ce hakan wajibi ne don bai wa mutane damar amfani da hakkinsu na ’yancin magana da samun bayanai.
Ta ce karin zai kara tsunduma mutane cikin talauci da kuma kawo nakaso ga harkar sadarwa a fadin Najeriya.
Kungiyar na rokon kotu ta bayar da umarnin dakatar da NCC, wakilanta ko kamfanonin sadarwa daga aiwatar da karin kudin.
Lauyan SERAP, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN), ya ce wajibi ne a tabbatar da adalci, bin doka da kuma yin la’akari da yanayin da mutane ke ciki, kafin yanke duk wani hukunci da zai shafi rayuwar jama’a.