Shugaban Kasar Senegal, Macky Sall, ya roki Jamus da ta ci gaba da girke dakarun sojinta a Mali, saboda rashin tabbas da ya mamaye kasar sakamakon janyewar dakarun Faransa.
Bayan gana wa da shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier a Dakar, Sall ya ce bai dace kowa ya gudu ya bar Mali ba, saboda haka yana da kyau dakarun Jamus su ci gaba da zama a kasar.
- Iyayen matashin da Hukumar KASTELEA ta ‘kashe’ suna neman hakki
- Boko Haram: Harin Bom ya hallaka jami’an tsaro 7 a Neja
Kasar Jamus na da sojoji 1,170 da ke aiki a karkashin dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali.
A makon da ya gabata ne Faransa ta sanar da shirin janye dakarunta da su ka shafe shekara tara suna yaki da ta’addanci a yankin Sahel daga Mali, biyo bayan sabanin da suka samu da hukumomin kasar a karkashin gwamnatin mulkin soji.
Hakan ya sa ministar tsaron Jamus, Christine Lambrecht, ta bayyana shakku a kan ci gaba da barin dakarun kasar a Mali bayan janyewar Faransa.
Lamarin da ya fara jefa shakku da tsoro a kasashen da ke makwabtaka da kasar Mali.