Some-somen sabanina
Da jiga-jigan Haurobiyawa
Shi ne kaiwa da komowa
Wajen sata da dira wawa
Na dade da alhinina
Baban-burin-huriyya
Ba ya nuna wariya
Al’umma yake bai wa kariya
Ba ruwansa da kulalliya
Balle adawa da makircin tsiya
Shara
Aikin da ya dumfara
Lallai sai an yi gyara
Ana duba bakin gatarin sara
Har a tara muku rarara
Kwashi-kwaraf da dukiyar kasata
Ashe bera na da sata
Daddawa ma na da wari
An yi ja-in-jar janye wuri
Bisa ingarma nake sukuwata
Al’umma sai a fahimta
Nagartar ayyuka aka lizimta
Keke-da-keke za a kwatanta
Fa’idoji sai mu rabauta
Har halin rayuwa ya inganta
A dai kiyaye dokoki
Masu keta doka a taka musu burki
Mun fasko mutanen kirki
Da masu kiren karyar carar carki
Lamura na daf da ban mamaki
Jajircewar jami’aina
Kai-kawon kara-kaina
Karambanin karkatar da kasafina
Lallaga laligar lallata lissafina
Karafunan karfa-karfan kugina
Share-sharen jibgin kazanta
Juyin shari’ar kasata
Ya cika ko’ina
Ko ina za a kaita
Matsalar ta sa an kuntata
Adadin adon adaka
Tudun adadun kuryar uwar daka
Suturu har da irin na Makka
Bayan an yi wanka
Sai dandasa kwalliya a saka
Ku dai jama’a
A daina ba’a
Mui fafutikar sana’a
Tare da neman sa’a
Mui biyayyar zaman da’a
Wadatar zuci da kana’a
Farfar da juna ai fara’a
Ai tarairayar biyayya ba a’a
Ko da a jam’in jama’ar jami’a
Inda masu neman ilimi ke kira’a
A inganta muhali
Shara ta karade babban fili
An shata harsashin kafa babban tubali
Daukacin ayyukan an musu fasali
Ana ta bin doka da doka misali
Masu mugun kulli
Sai a gyara hali
Mu zam masu tattali
Da dukiya ba a fatali
Fatara ai mata yankan kansakali
Masu danboto
Tuni an samu rahoto
Wasu sun dauki hoto
Na masu hadamar koto
Damin matsabbai sai an kwato
Madaurin tsintsiya
An sha daurin wuya
A daina tsiwa
Masu wawa ai musu tsawa
Lallai a kiyayi tsiya-tsiya
Sauyin sha’anina
Sunkurun sunkutar samarin-kusu
’Yan matan jaba su bi su
An damke masu burma asusu
Sanannen lamari ne a ganina
Mui wa kasa kakkarfan gini
Ba kiremn karyar sauyin launi
An fasko masu yi wa al’umma lahani
ci-ma zaunen damina da rani
Rini ya zama bi sa hani da umarni
Tanade-tanaden kundin kunshe tushe mulkin al’umma, tuni ya shimfida ka’idoji, wadanda in aka bi za a samu fa’idoji, amma tsawon shekaru sili da manuniyar sama aka shafe ana ta hauma-hauma, har ta kai ga an rasa makama. Wai duk da haka jam’iyya mai danboto da sanka jirge take shigar sunkurun sake darewa bisa karaga don jan ragamar al’umma, ta yadda za ta yi raga-raga da kasa.
Mai danboto dai ta yi taronta na jikkata jinkar DABARBARU A DABAI, ta yadda za ta nunke al’uma a baibai, musamman in ta jinko muku ’yan matsabbai.
Bisa la’akari da shekaru sili da mnuniyar dama da aka lakume wajen gudanar da mulkin mulaka’un DAMO-DA-KURA-DIYYA, ban ga alfanun hankoron fafutikar sake darewa karaga bayan tafka ta’asa a kwanon tasa, inda dimbin dukiyar kasa aka yi sama da fadi, har al’umma ta ji mummunan radadi. Yanzu sun bullo da sabon salon sole jiki da sabulun salo, wai sun fito fes, don fara karma-karmar hauma-haumar haramar handama. Sannan sun buge da hatsaniyar hadidiyar hadama.
Farfajiyar makaranta Dodorido da ke cikin Amintacciyar jaridar Haurobiya na nan kan manhajarta mara hajijiya, wajen nusar da al’umma, muhimmancin bin doka don kada kowa ya koka, sanan a kawar da juhala a tabbatar da dala, amma ban da DAFDALAR DAULAR DALAR DALA.
Karshen mai kwalama dai dole ne Haurobiyawa ku ce masa AHIR DINKA! CIM-BIN-KWALAM!
Ba za mu lamunta ba. Irin wannan kwan-gaba, kwan-baya. Burin masu hanakali bai wuce tabbatar da LULLUMIN LUMANA LULUM!
Kun ga ke nan nwannan manufar ce ta sa Gwamnatin Baban-burin-huriyya ke ta kara kaimin jadadda SAUYI YA SOMO DAGA SANSANINA. Ni kuwa na ce SAUYIN SHA’ANINA, shi zai ba ni damar yin SHAGALINA, amma ba shagaltuwa da babatu da buruntun butu-butun surutu rututu, har in zarta kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, wajen zubo bayanai al’amuran da ke wakana rututu.