Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iliya Damagum, ya ce ficewar Atiku Abubakar daga jam’iyyar ba abin mamaki ba ne.
Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidan gwamnati da ke Bauchi.
- An gano badaƙalar biza ta N500m da kama mutum huɗu a Legas
- Buhari ya min nasihar kula da talakawan Najeriya — Peter Obi
Damagum, ya ce irin wannan abu ruwan dare ne a siyasa, kuma yana da tabbacin cewa Atiku zai iya dawowa cikin jam’iyyar a nan gaba.
“Ba sabon abu ba ne, kuma ba zai zama na ƙarshe ba. Har yanzu muna sa ran zai dawo nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a 2023 a jam’iyyar PDP, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a ranar Laraba.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban mazaɓarsa da ke Jada, a Jihar Adamawa, ya ce ya fice ne saboda rikicin cikin gida da ke damun jam’iyyar.
Haka kuma, Atiku ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda jam’iyyar ke tafiya a yanzu, wanda ya ce ta kauce daga ainihin manufofi da aƙidun da aka kafa ta.