✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sauya shekar Mustapha Inuwa zuwa PDP cin amana ne —APC

Mustapha Inuwa shi ne Sakataren Gwamnatin Katsina da ya fi dadewa

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Shafi’u Abd-Duwab, ya ce sauya sheka zuwa Jam’iyyar PDP da tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, ya yi cin amana ne.

Abdu-Duwab wanda shi ne Sakataren Walwala na APC, ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsu da manema labarai ranar Lahadi a Katsina.

Mustapha Inuwa, wanda ya nemi takarar gwanan jihar karkashin APC, ya shelanta cewa ya sauya sheka  da APC zuwa PDP ne a lokacin da yake yi wa magoya bayansa jawabi a safiyar Lahadi.

Abdu-Duwab ya bayyana cewa, daukar matakin sauya sheka da Mustapha Inuwa ya yi alama ce ta rashin yarda da kaddara.

“Ina ganin addu’o’i da bayanan da ya yi a lokacin da ya sha kaye ba daga zuciyarsa ba ne.

“Yana daya daga cikin mutanen da Gwamna Aminu Bello Masari ya bai wa damar da ba kowa ya same ta ba; Don haka ya ce bai kamata ya ci amanar jam’iyya da Masari ba,” in ji shi.

Daga nan, ya nusar da Inuwa kan ya sani duk yadda ya kai da son zama gwamna idan ba da yardar Allah ba, babu wani mahaluki da ya isa ya dora shi kan wannan mukamin.

Ya ce duk da dai ba su ji dadin sauya shekar da Inuwa ya yi, amma suna da yakinin hakan ba zai yi wani tasiri ga jam’iyyarsu ba.