✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauya shekar Maman Taraba da kuma sake takarar Gwamna a 2019

Mai karatu ina fatan lokacin da kake karanta wannan makala ka gama jin cikakken jerin sunayen dukan wadanda za ka zaba daga dukan jam’iyyun siyasar…

Mai karatu ina fatan lokacin da kake karanta wannan makala ka gama jin cikakken jerin sunayen dukan wadanda za ka zaba daga dukan jam’iyyun siyasar kasar nan da za su fafata a babban zaben da ke tafe, kasancewar duk jam’iyyar da za ta shiga zaben ta tsayar da nata gwanin zuwa yanzu.

Kafin kaiwa ga wannan fage, na san mai karatu ba zai manta da sauye-sauyen sheka da ka-ce-na-ce da kai ruwa-rana da nuna halin ko a mutu ko a yi rai da aka yi ta samu  a tsakanin masu kwadayin mulki a kasar nan ba, musamman a cikin manyan jam’iyyun APC da PDP da ake kallon tsayawa takara cikinsu tamkar cin zabe ne.

Ba niyyar wannan fili ba ne ya kawo bayanin yadda aka yi ta samun karfa-karfa da nuna isa da kama-karya a siyasar ubangida daga shugabannin manyan jam’iyyun biyu ba, a shirye-shiryen fitar da gwanayen jam’iyyun, amma babban abin da ya bayyana a cikinsu bai wuce karin maganar da Hausawa kan yi ta “Kowane gauta ja ne, sai in bai sha rana ba.” Ma’ana kowace jam’iyya tsakanin APC da PDP shugabanninta sun jarraba irin tasu karfa-karfar, walau daga shugabanni na kasa ko na jiha, wato gwamnonin jihohi, musamman wadanda suke kammala wa’adinsu na karshe a badi.

Mai karatu bari mu tafi inda makalata take so ta mai da hankali a yau. Na san dai kana sane da cewa zuwa yanzu Hajiya A’isha Jummai Alhassan, tsohuwar Ministar Harkokin Mata da ake yi wa lakabi da Maman Taraba, ita ce ’yar takarar Gwamnan Jihar Taraba a karkashin Jam’iyyar UDP. Jam’iyyar da ta canja sheka zuwa cikinta, bayan da Shugaban APC na Kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ki amincewa a tantance ta a matsayin ’yar takarar APC a neman kujerar Gwamnan Jihar Taraba, ita da Ministan Sadarwa, Barista Adebayo Shittu, wanda shi ma ya so tsayawa takarar Gwamnan jiharsa ta Oyo a zaben da ke tafe.

Oshiomhole ya ce APC ta ki amincewa ta tantance Ministan Sadarwa ne sakamakon rashin takardar shaidar hidimar kasa da kuma lashe zaben shiga Majalisar Dokokin jiharsa, wanda Ministan ya zabi ya tafi wakilci a Majalisar Dokokin, yana ganin ya fi muhimmanci, hanzarin da Oshiomhole ya ce ba ya da inganci a gaban shari’a, kasancewar dokar kasa ta ce tilas ne ga duk wanda ya cancanta ya tafi hidimar kasar ta NYSC, muddin ya kammala karatunsa na digirin farko ko na babbar takardar shaidar difloma face sai shekarunsa sun yi yawa. Wannan kuma kila saboda APC na jin tsoro kada a karshe jam’iyyar adawa ta kalubalanci zaben a kotu, ana kuma iya kwace shi. Ko a kwanakin baya Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta ajiye mukaminta bisa zargin takardar shaidar jabu ta hidimar kasa.

Ita kuwa tsohuwar Ministar Mata babban laifinta shi ne rashin cikakkiyar biyayya, inda Oshiomhole ya kafa hujja da cewa a baya an ji ta tana fadin wasu maganganu a kan wani dan takarar neman Shugaban Kasar nan. Idan mai karatu bai manta ba koda a cikin wannan shafi a bara, na bi sawun irin kalaman da Hajiya A’isha Jummai ta yi a lokacin da ta kai ziyarar gaisuwar Sallah ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar da a lokacin yake jigo a cikin APC, amma kuma ana ta rade-radin zai iya sauya sheka zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.

An ruwaitota tana cewa muddin Atikun zai tsaya takarar Shugaban Kasa, to kuwa za ta je ta ce da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari “Ga mukaminka na Minista zan bi Alhaji Atiku Abubakar don in taimaka masa ya kai ga nasara, tana mai karawa da cewa, don ni ba zan zama munafuka ba.” Wani hanzari da Maman Taraba ta bayar a wancan lokaci shi ne Alhaji Atiku ubangidanta ne a siyasa da ba ta da kamarsa, ita kuma ba ta iya munafunci irin na ’yan siyasa ba ballantana ta raba kafa a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku.

Wancan jawabi na Hajiya Jummai ya yamutsa hazo sosai a wancan lokaci, bisa irin yadda wadansu suka yi ta kiraye-kirayen a sallame ta daga mukaminta na minista. Amma dai Shugaban Kasar ya ki daukar mataki sannan ya yi gum da bakinsa, ashe, ashe wata na tafe. Bayan wancan hani da APC ta yi mata, yanzu ta ajiye mukaminta na Minista sannan ta fice daga APC zuwa UDP, inda take yunkurin cika burinta na zama Gwamnar Jihar Taraba.

Sannan ta ba da sanarwar cewa ta fice daga APC tare da wadansu ’yan Majalisar Jihar su 7 da dukan shugabannin mazabu 169 da na kananan hukumomin jihar 16, da dukan shugabannin kwamitin zartaswa na jihar, sun bar APC, sun koma UDP. Tana mai ba da hanzarin cewa “tunda dai ban cancanci tsayawa takarar Gwamna a Jam’iyyar APC ba, to kuwa ban cancanci ci gaba da tsayawa minista a cikin gwamnatin APC ba.”

A ra’ayina a lokacin da ’yan siyasar kasar nan suke neman inda za a yi da su da sunan yadda za su taimaki jama’arsu, (ko wannan ikirari gaskiya ne?). Ni ma na yarda Hajiya Jummai ba ta ga ta zama ba a Jam’iyyar APC. Wadansu ’yan siyasa da ma ba su taba kusantar tsayawa takarar neman ko da dan majalisar dokokin jiha ba, su kan rude a kan sai sun yi takarar Gwamnan jiha, ballanta Hajiya Jummai da ba sabuwar yankan rake ba ce a siyasar Najeriya, matar da a zaben 2015 aka kyautata zaton ita ce ta lashe zaben Gwamnan Jihar Taraba, amma aka yi mata karfa-karfa irin ta kabilanci da addini da har a kotu aka kwace zaben. Me zai sa yanzu ta ci gaba da zama a jam’iyyar da za ta binne ta da mutanenta. Sai dai kuma ban san yadda za ta kare da irin dubban magoya bayan Buhari da yake da su a jihar ba. Duk da haka tunda dai ta dauko sabuwar jam’iyya don ta gwada sa’arta, ni ma daga nan ina cewa Maman Taraba Allah ba da sa’a.