✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh

Wannan lamarin shi ne mafi muni cikin hadurran jiragen sama da suka faru a kasar cikin shekaru da dama.

Kimanin mutum 16 sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka, babban birnin kasar.

Haɗarin jirgin saman yaƙin ya kuma yi sanadin jikkatar gommai, wanda ya kasance guda daga cikin haɗɗura masu muni da ƙasar ta gani a baya-bayan nan a fannin jiragen sama.

Wani mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na AFP da ke wurin ya ce ya ga jami’an kashe gobara suna kwasar daliban da suka jikkata yayin da sojoji ke taimakawa wajen zakulo mutane daga cikin baraguzan jirgin da ya fadi.

Fiye da mutane 100 ne suka jikkata a hadarin, inda akalla 83 ke karbar magani a asibitoci daban-daban, in ji wani jami’i a ofishin gwamnatin kasar, Muhammad Yunus.

Bayanai sun nuna cewa waɗanda suka jikkata mafi yawansu ɗalibai na karɓar kulawar likitoci, yayinda wasu yayi munin da sai anyi musu gagarumar tiyatar sauya hallita.

Jirgin na F-7 BJI da aka kera a kasar Sin ya tashi ne da karfe 1:06 na rana (07:06 GMT) kuma ya faɗi mintuna kaɗan bayan da aka saki ɗaliban daga ajujuwansu don fita tara a harabar makarantar mai suna Milestone School and College.

Faya-fayan bidiyo sun nuna yadda iyayen ɗaliban suka isa filin makarantar a ƙiɗime, don neman yaransu, amma wasu anan suka ci karo da gawargwakin yaransu.