✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biden na hawa jirgin shekara 30, Najeriya ta yi watsi da jirgin shekara 19

Sayen sabon jirgin shugaban ƙasar ya haifar da cece-kuce a Najeriya.

Har yanzu dai Fadar Shugaban Ƙasa, ba ta ce uffan kan kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayo sabon jirgin shugaban ƙasa, ƙirar Airbus A330 ba, wanda hakan ke ci gaba da yamutsa hazo a Najeriya.

Sai dai wani sabon rahoto ya gano yadda shugaban ƙasar Amurka ke hawa jirgin da aka shafe shekar 34 ana amfani da shi.

Wannan ya biyo bayan yadda gwamnatin ta ƙaddamar da sabon jirgin shugaban ƙasa kirar Airbus A330, ba tare da bayanin yadda aka samu kuɗin sayen jirgin ko kuma sahalewar Majalisar Dattawa ba.

An dai fara cece-kuce kan sayen jirgin ne bayan wanda aka saya tun zamanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya fara bayar da matsala a tafiye-tafiyen da aka yi da shi zuwa ƙasashen Saudiyya, Netherlands da kuma Afrika ta Kudu.

Wasu bayanan sirri daga fadar shugaban ƙasa na cewa an sayi sabon jirgin ne kawai saboda wanda shugaban ke hawa ya shafe shekara 19 ana amfani da shi.

Sai dai wani sabon bincike ya nuna yadda shugaban Amurka ke amfani da jirgin saman da ya shafe shekaru 34 ana amfani da shi, iyaka a kai shi wajen gyara da sauransu.

Fadar shugaban ƙasa, ta sha nanata cewa lalacewar jirgin da shugaban ƙasa ke amfani da shi abin kunya ne kuma bai dace a ce ana ci gaba da amfani da shi ba.

Sai dai abin da ya fi ɗaure wa jama’a kai, shi ne yadda aka sayi jirgin da kuma inda aka samo kuɗaɗen.

Har yanzu dai babu wani ingantaccen jawabi daga fadar shugaban ƙasa kan sayen jirgin.

A ranar Talata ne Shugaba Tinubu, ya tafi ƙasar Faransa a sabon jirgin da aka saya masa.

Kakakin Tinubu, Bayo Onanuga ne, ya sanar da hakan a shafinsa na X (Twitter), a ranar Talata.