✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauya dokar haraji: ’Yan Arewa a majalisa sun nuna damuwa

’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun nuna damuwa cewa kudirorin Shugaba Tinubu na sake dokar haraji zai kara gurgunta tattalin arziki da matsin rayuwa da…

’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun nuna damuwa kan wasu kudirori hudu na sake fasalin dokar haraji a yayin da majalisar dokoki ta kasa take ci gaba da nazari a kan kudurorin.

Sun yi wannan jawabi ne a zaman tattaunawa da majalisar ta yi da mambobin kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji a ranar Litinin.

Kudurorin gyaran da ake shirin yi wa rabon haraji (VAT), da suka haifar da cece-kuce su ne: Dokar Harajin ta 2024, wadda ake sa ran za ta samar da tsarin kasafin kudin haraji a kasar.

Na biyu, Dokar Kula da Haraji, wadda za ta samar da tsayayyen tsari na doka game da duk harajin da ke cikin kasa tare da rage rikice-rikice.

Sauran su ne: Dokar Kafa Haraji , wadda za ta soke dokar Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) da kuma kafa Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Najeriya (NRS).

Na hudu ita ce dokar kafa hukumar tattara haraji ta hadin gwiwa, wadda za ta samar da kotun sasanta rikicin haraji.

Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) da gwamnonin jihohi sun bukaci shugaba Tinubu ya janye kudirin don ci gaba da tuntubar juna.

Har ila yau, shugabannin Arewa da suka hada da sarakunan gargajiya da ’yan majalisar dokoki, sun nuna rashin amincewarsu, inda suka yi zargin garambawul din da ake shirin yi ya karkata ne wajen cutar da yankin.

Amma duk da haka, Tinubu ya ce ya kamata ta ci gaba da aiki a kai, yana mai jaddada cewa tattaunawar da ake yi tana ba da damar yin amfani da bayanai da gyara ba tare da an janye kudirin ba.

A zaman da aka yi a ranar Litinin, ’yan majalisar Arewa da suka hada da Honorabul Yusuf Adamu Gagdi da Ahmed Jaha Babawo da Zainab Gimba da kuma Zakariah Dauda Nyampah sun bayyana damuwarsu game da illar da kudurorin za su yi wa yankin.

Sun yi iƙikrarin cewa tattalin arzikin yankin, wanda ya riga ya raunana a sakamakon matsalar rashin tsaro da rashin aikin yi, na iya kara lalceaw a karkashin gyare-gyaren da ake shirin yi.

Sai dai tawagar fadar shugaban kasa na sake tsarin harajin ya kawar da fargabar, inda ta ce rabon kudin harajin na yanzu ya fifita wasu jihohi ’yan kadan, kuma hakan rashin adalci ne ga wasu.