Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce za su iya gamawa da matsalar ta’addanci, tayar da kayar baya, ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane cikin kankanin lokaci muddin jama’a suka ba su hadin kan da ya kamata.
Ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da ‘yan jarida bayan wata ganawa da Shugaba Buhari kan kokarin da sojojin ke yi don yaki da miyagu a yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Ya ce bayar da bayanan da suka kamata ga sojoji da sauran jami’an tsaro kan maboyar batagari zai taimaka matuka wajen kawo karshen kalubalen tsaron.
Buratai ya ce duk da cewa aikin samar da zaman lafiya ba abu ne mai sauki ba, sojoji na samin galaba kan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sauran masu tayar da kayar baya a yankin.
Ya ce, “Kusan kaso 99 cikin dari na ‘yan ta’addar nan ‘yan Najeriya ne, kaso 100 na masu garkuwa da mutane kuma ‘yan Najeriya ne. Kun ga ke nan aikin ba na sojoji ba ne kadai. Kowa na da irin gudunmawar da zai bayar wajen yakar matsalar.
“Amma idan muka nade hannuwanmu muka ci gaba da korafi da zargin jami’an tsaron da ke yakin ba tare da yin abin da ya dace ba, ba na tunanin za a iya samun nasarar da ta kamata”, inji Buratai.
Ya kuma ce yanzu ba a samun yawan kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma satar shanun da suka addabi yankin tare da yin barazana ga manoma a gonakinsu a baya, yana mai cewa hakan na da nasaba da jajircewar da jami’an tsaron ke yi.
Ya ce sojojin za su tabbatar cewa nasarar ta ci gaba har bayan lokacin damuna, kuma babban abin da suke bukata shi ne hadin kan jama’a ta hanyar samar da bayanan sirri.
Yankin Arewa maso yammacin Najeriya dai na fama da matsalar ‘yan bindiga ne da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, yayin da a yankin Arewa maso Gabas kuma matsalar tayar da kayar baya da ta’addanci ta ki ci ta ki cinyewa cikin sama da shekaru goma.