✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura kiris a kashe ni tare da Sardauna

Alhaji Aliyu Shehu Maradun wanda marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahamdu Bello ya sanya wa sunan dan-kwadangwame bayan ya gano cewa sun fito daga tsatson Shehu…

Alhaji Aliyu Shehu Maradun wanda marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahamdu Bello ya sanya wa sunan dan-kwadangwame bayan ya gano cewa sun fito daga tsatson Shehu dan Fodiyo ne, ya yi aiki da marigayin a matsayin direba, kuma a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana wasu abubuwan da ya sani game da Sardauna da yadda suka rayu tare da shi:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka? 

Asalina ni daga tsatson Mujaddadi Shehu Usman dan Fodiyo, ta salsalar Muhammadu Bello sai Sarkin Musulmi Abubakar Atiku, sai Sarkin kayan-Maradun, Muhammadu Mu’allayidi, sai Sarkin kaya Attahiru, sai Sarkin kaya Moyi, sai Ahmadu Marafa Makwashe, Hakimin Tsohuwar Maradun sai ni Aliyu Shehu Maradun. daya daga cikin matana uku jikar Sarkin kaya Ibrahimu ne, shi ya haifi mahaifiyarta. daya daga cikin matan nawa zuriyar Abdullahin Gwandu ne. Matana uku, biyu na Sakkwato, daya na Gusau sannan ina da ’ya’ya 20, maza 14 da mata 6. Mahaifina Ahmadu Marafa Makwashe ya yi Hakimcin Maradun Tsohuwa. Amma ina amfani da sunan kawuna da ya sani a makaranta ne, domin an ba da doka a fadar Sarkin Musulmi cewa kowane Hakimi ya sanya ’ya’yansa a makarantar boko. Na fara karatun elemantare ko firamare a 1957 lokacin da Sarauniyar Ingila ta zo Najeriya. Da na gama aji hudu a Maradun sai muka yi jarrabawar zuwa babbar firamare, aka kai ni Kwatarkwashi a 1961 muka yi aji bakwai. 

Yaya aka yi ka fara haduwa da Sardauna? 

An aiko da takarda ce daga Sakkwato ta hannun Alhaji Sani Dingyadi wanda babban kansilan ilimi ne cewa duk wanda ya kare firamare bai tafi wani wuri ba, ana nemansa a Sakkwato. Mu 75 muka je Sakkwato, aka ba ni lamba ta 25 cikin wadanda jami’in ilimi na Lardin Sakkwato, Alhaji Isma’ila Ahmed, Dallatun Zazzau suka yi wa jarrabawar tantancewa. Cikin tambayoyin har da ko muna iya karantarwa na ce, eh. A lokacin in ka kammala makaranta sai a kai ka wata makaranta a matsayin karamin malami (Pupil-Teacher.” Da aka kammala sai aka kira ni, aka ce mota zan tuka, na ce ban iya mota ba, aka ce za a koya min. Aka ce in jira a gindin wani madaci a Gidan Gwamnan Sakkwato ni da Abdulkadir kaura yana nan a kaura amma ya samu lalura yanzu ba ya gani. Aka ce mu tafi mu shiryo za a kai mu Kaduna da karfe 2 na rana, mu hadu a inda ake kwallon hannu na “Fibes” a filin Sukuwa na Sakkwato. Aka sa wani direba mai suna Na-Madawo ya kawo mu Kaduna, muka kwana a Gusau, daga garin Maska ba kwalta har Funtuwa sai washegari karfe 2 muka isa Kaduna. Aka gaya wa Babban Sakataren Sardauna, Alhaji Hassan Lemu, ya fito ya je ya yi mana iso wurin Sardauna aka ce mu shiga. Sardauna ya tambaye mu sunanmu da gidanmu na fada masa, a lokacin nban san ni jinin Shehu dan Fodiyo ba ne, ban san ina da alaka ta jini da Sardauna ba. Na ce masa mahaifina magatakarda ne na wani hakimi a lokacin, Abdulkadir kaura ya fadi saunansa da inda ya fito. Sardauna ya ce a kai mu gidan Sarkin Fada aka ba mu daki aka ce gobe da safe za a kai mu Ma’aikatar Ilimi da ofishin bIO a Titin Sakkwato, kusa da Gidan Gwamna a Kaduna don koyon mota. 

Mun yi wata uku muna koyo a motar gwamnati kirar Land Rober inda Sa’idu dan-Kwara wani tsohon soja da ya yi Yakin Duniya yake koyar da mu. Sai wani Bature ya ce mu tuka domin ya gwada mu, amma aka ce ba mu ci ba sai mun kara kwana 29 ko wata daya. Bayan na samu nasara sai Sardauna ya sa aka kai ni wurin wani Baturen Holland a Kamfanin UTC domin a koya min gyaran mota. Bayan wata uku aka ba ni satifiket na dawo muka ci gaba da rangadi da Sardauna. An dauke ni aikin tuki a ofishin Firimiya a kan albashin Fam 11 da sule 10, a 1964.

Ya aka yi kai da Sardauna kuka san ku ’yan uwa ne?

Lokacin za mu tafi gonar Sardauna a Bakura, mun yi zango a Gusau, da Sarkin kayan Maradun, Muhammadu Tambari ya hango ni a kan shimfida kusa da Sardauna, sai ya ce in an tashi yana son ya gan ni. Bayan nan sai Sardauna ya ce sarakunan Bungudu da Maru da Maradun da Mafara su tarbe shi washegari a iyakar kasarsu. Sai muka tafi muka kare da Maru, muna zuwa Maradun daidai Gidan Taba muka iske sarakunan, Sardauna ya ce yana ji kamar yana garin Rabah, domin ya iso inda ’yan uwansa suke. Ya ce ina Marafan kaya, wanda asalin iyayensu daya da wadanda suka haifi iyayena, sai ya ce ga shi. Sai ya ce, shi kadai ne ya girme shi a Maradun, amma saura duk kannensa ne da ’ya’ya da jikoki. Sai ya ce da Sarkin kaya idan mun isa Bakura zai aiko musu da sako, ya ce da shi da Marafan kaya su jira nan, suka yi ban-kwana. Da Sarkin Bakura ya tarbe mu sai Sarkin Mafara ya koma, muka wuce gona sai aka ba ni sako in kai wa Sarkin kaya. Da na kai sai ya ce zai bi ni mu koma don ya yi godiya da yaronsa Magayaki, na dauke su muka koma Bakura na shiga na yi masa iso, Sardauna ya ce ya shiga, suka gaisa. Sai Sardauna ya ce ka ga wani yaro na dauko daga garinka. Sai ya ce ai yaron nan jikanka ne, sai Sarkin kaya ya fadi asali har zuwa Sarkin Musulmi Abubakar Atiku. Sardauna ya ce in mayar da shi,  da na dawo, ya bar sakon yana kira na. Sai ya kira shugabanmu Ali Sarkin Mota ya ce ga danka nan in ya yi kirki kai ne, in ya lalace kai ne, tun sannan na dauki Ali Sarkin Mota a masayin uba. 

Bayan da Sardauna ya gane ni jinin Shehu dan Fodiyo ne, sai ya ce ba ni da darajar da za a kira ni Shehu, ya ce daga yau sunana dan-kwadangwame. Na zama dan cikin gida sosai daga cikin mu direbobi 12 a karkashin Ali Sarkin Mota. 

Yaya aka yi Sardauna ya rasu jim kadan bayan rabuwarku?

Sarduana ya dawo daga umara a cikin watan azumi ya sauka ranar Laraba a Kano inda Ali Sarkin Mota da Sa’idu Bidda da ni muka je dauko shi. Ya sauka da karfe 2:45 na rana, ya ce a je masauki bai fito ba sai wurin karfe 5, ni da wadansu mutum biyu muna zaune, sai ya fito ya ce, dan-kwadangwame. Na ce ranka ya dade sai ya ce me ke fitowa da Asuba daga Gabas, sai na ce alfijir ya ce a’a. Na ce Gamzaki ya ce a’a. Na ce, to ranka ya dade wallahi ban sani ba. Sai ya ce wannan ne shaidar ba mu Sallar Asuba sai rana ta fito. Sai ya tambayi wadanda muke zaune mu biyu ko da wanda ya sani? Suka ce ba su sani ba, sai ya ce duk ba mu Sallah sai lokacin da muka ga dama. Sai ya ce wanda yake son ya ga abin nan ya tashi da Asuba ya yi Sallah. Ran nan na farka tun karfe 12:30 na dare har karfe 4 ana kokarin a yi Sahur sai na ga wannan abin kamar tabarya a sama mai haske. Sai na ce ina ganin wannan ne abin da Sardauna ke magana. Bayan Sahur aka yi Sallah da safiya ta waye sai Sardauna ya fito za mu tafi Kaduna ran Alhamis, ana gaisuwa sai na ce, ranka ya dade na ga abin nan. Sai ya ce me na gani, sai na ce na ga wani abu kamar tabarya mai haske, sai ya ce eh lallai ka tashi ka yi Sallah da wuri, amma Allah Ya sauwake, na ce amin. Da muka nufi Kaduna, mun kai Rigachikun inda muka iske masu tarba kafin mu wuce gida. Da muka isa gida sai aka kawo wata mota cike da Alkur’anai da carbi da atamfofi da alawayyo wadanda ake ba wadanda suka Musulunta da mutane. Muka je masallacin Rigachikun inda a da yake Sallar Juma’a kafin a gina Masallcin Sultan Bello a Unguwan Sarki, Kaduna, wajen saukar Alkur’ani don an kai karshen Tafsiri. Da muka dawo gida sai Samuel Akintola Gwamnan Jihar Yamma ya samu labarin Sardauna ya dawo sai ya bugo masa waya, ya ce akwai magana da yake son yi masa amma ba a waya ba, don haka ya aiko masa da mota gobe da safe Juma’a a dauke shi a Filin Jirgin Saman Kaduna. Da safe ni da Yando Argungu aka ce mu bi Ali Sarkin Mota mu je mu dauko shi a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Lemu. Ashe dan tawaye Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu ya aje mota kirar Land Rober a kofar gidan Sardauna tun yamma inda aka gina dakin taro na “Gidan Arewa” ya biyo mu ba mu san ko wane ne ba. Da muka isa filin jirgin, sai ya je mangwarori ya tsaya, da muka dauko Akintola, sai suka shige cikin ofis. Ni kuma ban sani ba, sai na je wani daki, ashe suna kusa da dakin suna hira, sai na ji Akintola ya ce masa, kana da labarin sojoji za su yi bore? Sai Sardauna ya ce ai kai ne Sarkin Yakin NPC sai ka yi maganin borensu. Sai ya ce ga jirgi nan ya kawo su fita su bar kasar. Sai Sardauna ya ce ko yadi guda bai barin kasar nan da sunan wani zai kashe shi. Ya ce duk inda kake so cikin kasashen makwabta zan ba ka takarda ka sauka, suka yi ta hira, sai na yi maza na bar dakin. Da suka gama maganar muka mai da shi filin jirgi sai ya kawo Fam 20 ya ba mu muka dawo. Ashe Sardauna ya samu takarda cewa za a kashe shi ranar Juma’a.

Da yadawo juma’a daidai dorawar da aka gina dakin taro na Gidan Arewa, sai ya ce a kawo kujera ya zauna har La’asar, ya ce duk wanda yake son kashe shi, ba sai ya shiga cikin gida ba, ga shi a fili, ya yi La’asar ya dawo. Kafin karfe 5 aka ce ya tashi ya shirya buda-baki. Na tafi gidana domin na yi aure a lokacin, gidana na gefen gidan Limamin Masallacin Sultan Bello, Kaduna, inda ma’aikata ke zama. Gidan na tsakanin gidan Alhaji Sani One-Minute da gidan Ali Sarkin Mota. Muna zaune a gidan da wadansu kamar Yakubu Tafawa balewa, wanda ake ce wa Baba don sunan mahaifin Tafawa balewa yake da shi da sauran mutane, bayan Magriba sai na koma gidan Sardauna, domin in yi masa barka da shan ruwa da azumi. Da muka zauna muna fadanci, sai mutane hudu suka shigo da Ali Akilu da M.D. Yusuf da Birgediya Ademulegun da Yusuf Balanta, suka tashi suka wuce dakin taron, Sardauna ya bi su, ni ban san me suka ce ba, suka fito suka tafi. Bayan minti 25 sai suka dawo amma ban da Birgediya Ademulegun, suka sake shiga suka fito, sai Sardauna ya yi dabarar kawar da hankalinmu, ya ce dan-kwadangwame kira min Ali Sarkin Mota a dakinsa wato ‘boy’s kwata.” Da ya zo sai ya ce Ali motoci suna lafiya, ya ce eh, sai ya ce da Ali Sarkin Mota da Sa’idu Bida da ni za mu tafi Sakkwato ranar Lahadi. Mutane suka ci gaba da yi masa barka da shan ruwa, yana ta ba da kyaututtuka. Da karfe 11 na dare sai na ce “Ranka ya dade, ka zama lafiya” sai ya ce “Ango kake, sai da safe,” domin lokacin bai dade da yi min auren fari ba, kuma iyakar maganata da shi ke nan. Ina kwance a gida, sai matata ta tashe ni da karfe 2 na dare ta ce an yi harbi, amma ni ban ji harbin farko ba, sai aka kara sau biyu. An yi harbin ne daga kan titin jirgin kasa da ke gefen gidan. Sai Umar mai aiki a gidan Sardauna ya ta da jiniya, sai ni da Audu dan Kini matumin Kazaure da Mamman Bakura mai kai wa Sarduana abinci da Alhaji Sani One-Minute ya dauko bindiga sai wani ya ce masa ya mai da bindiga mu je mu gani ko ’yan Action Group na siyasar Awolowo ne suka zo su kashe Sardauna, idan suka gan mu, mu za su fara kashewa. Sai ya mayar da bindiga muka kama hanya zuwa gidan Sardauna, mun kai gidan Micheal Audu Buba, Wazirin Shendam, kuma Minista, sai muka ga wutar gidan ta dauke, ashe duk inda muke sojoji ne a kwance. An dauki mota Land Rober an aje ta wajen gidan Alhaji Isa Kaita, an kunno wutar. Sai ga wani Abdulkadir dan Riji mai aikin gadina, sai muka ce muna lura da yanayi ne, mu kula kafin mu kusanci gidan, sai ya wuce mu, bai yi yadi dari tsakaninmu ba sai ba sai aka harbe shi a kafa, sai ya ja gindi ya dawo, sai wata mota ta taho ashe ma’aikacin ofishin Sardauna ne aka yi waya baya nan, sai aka ce in ya dawo a ce ya zo da wani fayil. Mutumin Bazazzagi ne ya je Zariya da ya dawo sai ya nufo gidan Sardauna, shi kuma bai san abin da duniya ke ciki ba, don ba a rufe hanyar Zariya zuwa Kaduna ba. Ya wuce mu, ya kai daidai gidan Sardauna mun aza yana magana da su ne, domin ko kashe mota da wutarta bai yi ba, suka harbe shi, nan ya mutu da suka gaji da ganinmu, sai suka rika yin harbi a sama muka gudu. 

 Kun yi aiki a zamanin da ba almundahana, me kake yi bayan da ka yi ritaya?

Mun yi aiki tukuru da gaskiya, amma ina da matsala domin gidan da nake ciki a Sakkwato na gwamnati ne mai dakuna biyu da kicin da bayi, tun 1991 nake ciki har na yi ritaya. Amma a yanzu an ce za a sayar mana, amma wai ni ba dan Jihar Sakkwato ba ne, ba za a sayar min ba, wai ni dan Jihar Zamfara ne. Ni direban Sardauna kuma zuriyar Shehu dan Fodiyo. Kuma ko an ce min in biya kudin ba ni da su, domin haka nake rokon Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III da Gwamna Aminu Tambuwal su yi min kyautar gidan, domin gidan da matata dayar take ciki a Zamfara shi ma na haya ne ba nawa ba ne. Ana son sayar da gidan ne a kan Naira miliyan biyu da rabi a biya cikin watanni. Alhali fanshona Naira dubu shida da dari bakwai da biyar da kuma kwabo shida ne kowane wata.