✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro

Ministan ya ce shugabanni tsaro sun bayar da tabbacin kawo ƙarshen matsalar tsaro a 2025.

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji.

Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025.

“Shugaban ƙasa na cewa yaushe matsalar tsaro za ta ƙare, saboda lokacin da ya kamata ta ƙare ya yi.

“A wani zama da muka yi da shi da shugabannin hafsoshin tsaron, an tattauna sosai, kuma shugaban ya ce su faɗa masa yaushe matsalar za ta ƙare, suka ce da yardar Allah zuwa ƙarshen shekarar nan,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Sun ce ko matsalar ba ta ƙare gaba ɗaya ba, to za a ga sauƙin da kowa zai gani ya kuma ji daɗi.”

A wani taron da aka yi tare da shugabannin tsaro, Badaru, ya ce Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa yana tsammanin matsalar tsaro za ta ƙare kafin ƙarshen shekara mai zuwa.

Hakazalika, ya ce idan matsalar ba ta ƙare, gwamnatin za ta ɓullo da sabbin dabaru domin murƙushe ta’addanci a yankin da ma Najeriya baki ɗaya.

A yayin tattaunawa da BBC Hausa, Ministan ya bayyana cewa duk da a yanzu ba a kama Turji ba, amma suna da labarin ya fara guje-guje, kuma nan ba da jimawa ba zai shiga hannu.

Ministan ya tabbatar da cewa tsare-tsaren da Gwamnatin Tarayya da hafsoshin tsaro suke aiwatarwa, za su kai ga gagarumar nasara wajen inganta tsaro a Najeriya.