✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saukin yin kasuwanci: Yadda Gombe ta yi zarra tsakanin jihohin Najeriya

An bayyana Jihar Gombe a matsayin wacce ke kan gaba cikin jihohin Najeriya 36 ta fuskar saukin yin kasuwanci. Bayanin hakan na kunshe ne a…

An bayyana Jihar Gombe a matsayin wacce ke kan gaba cikin jihohin Najeriya 36 ta fuskar saukin yin kasuwanci.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da Babban Daraktan Watsa Labarai na Gidan Gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya yi wa ’yan jarida a Gombe ranar Juma’a.


Ya ce matsayin da aka bai wa Jihar na kunshe a cikin sakamakon ‘Binciken Jihar da ta fi Saukin Gudanar da Harkokin Kasuwanci’ wanda Kwamitin Kula da Muhallin da ke Bayar da Damar Kasuwanci cikin Sauki na Fadar Shugaban Kasa (PEBEC) ya fitar.

A cewarsa, sakamakon shi ne matsayin rahoton Jihohin da yanayin da suke ciki a yanzu yake jan hankali da karfafa gwiwar kanana da matsakaitan harkokin kasuwanci.

Sakamakon binciken da Aminiya ta samu dai ya nuna Jihar Sakkwato ita ce ta biyu sai Jihar Jigawa ta uku yayin da Akwa Ibom ta zama ta hudu.

Binciken ya ci gaba da cewa batutuwan da aka yi la’akari da su a rahoton sune ababen more rayuwa da tsaro da kamanta adalci da damar samun bayanai da yanayin kula da abubuwa da ma samun masu aiki da ke cikin shiri.