Kasar Saudiyya a ranar Alhamis ta ce a karon farko, za ta tura mace zuwa Duniyar Wata a shekarar 2023 mai kamawa.
Hukumar Kula da Sararin Samaniyar kasar ce dai ta bayyana hakan inda ta ce ta bullo da shirin ne domin ta ba ’yan kasarta damar gogewa a doguwa da kuma gajeriyar tafiya a duniyar.
- Hira da Matashin Da Ya Kera Mota a Kano
- Yadda ’yan damfara suka wawushe sama da N500m daga asusun banki
Kamfanin Dillancin Labaran Kasar (SPA) ya rawaito cewa kumbon farko da zai tashi zuwa sararin samaniya a 2023 zai kunshi ’yan sama-jannati biyu, cikinsu har da mace daya, sai dai bai yi karin haske ba a kan haka.
“Wannan zai kafa wani muhimmin tarihi inda a karon farko za mu aike da mace zuwa sararin samaniya,” inji SPA.
Kamfanin ya ce nan da ’yan watanni masu zuwa gwamnatin kasar za ta fitar da cikakkun bayanai kan hanyoyin da za a bi wajen aikewa da mutanen.
A ’yan shekarun nan dai, Saudiyya ta yi wa dokokinta da dama kwaskwarima tare da yin sassauci a kan wasu manufofinta da suka ba mata karin dama.
Ko a 2018, kasar, a karon farko ta ba mata damar tuka mota bayan shafe tsawon shekaru ba su samu damar yin hakan ba. (NAN)