Gwamnatin Kasar Saudiyya ta fara tattaunawa da kamfanin Aston Martin mai kera motocin tsere da na alfarma domin sayen hannun jarin Dala miliyan 243.5.
Kamfanin Aston Martin da ke kasar Birtaniya shi ne ke kera motoci masu daukar ido da ke fitowa a fina-finan James Bond.
- Iyalan fasinjojin jirgin kasan Kaduna za su tare a ofisoshin gwamnati
- An kama shi kan azabtar da ’yar aiki da wuta kan keken ’ya’yansa
Mujallar kasuwancin ta Financial Times ta ce kamfanin na neman masu zuba jari ne domin samun kudaden da zai kera wasu sabbin nau’ikan motocinsa.
Mujallar motoci ta Autocar ta kara da cewa kamfanin yana tattauanwa da wani kamfanin zuba jari a kasar Amurka da nufin kara karfin jarinsa.
Aston Martin dai ya ki tabbatarwa ko kore rahoton cinikin tsakaninsa da Hukumar Zuba Jari ta Kasar Saudiyya.
Bayanai sun nuna bayan bullar labarin cinikin a ranar Alhamis hannun jarin kamfanin da ya karye da kashi 20 cikin 100 a farkon yinin ya ragu zuwa kashi tara cikin 100.
Tun bayan fara sayar da hannun jarinsa a 2018, Aston Martin ke fama da matsaloli; A 2022 kadai hannun jarinsa ya karye da kashi 68 cikin 100.
A watan Janairu, kamfanin ya danganta karancin samun ribarsa a kan jinkirin jigilar motocinsa na tsere samfurin Valkyrie.
Amma a ranar Alhamis ya ce ya kara karfinsa na kera Valkyrie, ya kuma ba wa masu zuba jari tabbaci cewa zai fito da sabbin nau’ukan motocinsa a 2023, karkashin jagorancin sabon shugaban kamfanin, Amedeo Felisa.