✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude masallatai a Saudiyya

Kasar Saudiyya na shirin janye dokar kulle da ta sanya a duk fadin kasar daga ranar 21 ga watan Yuni mai kamawa. Ma’aikatar Harkokin Cikin…

Kasar Saudiyya na shirin janye dokar kulle da ta sanya a duk fadin kasar daga ranar 21 ga watan Yuni mai kamawa.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta ce sassaucin bai shafi biranen Makka da Madina ba wadanda za su ci gaba da zama a rufe.

Sanarwar ta ranar Talata na zuwa ne bayan kasar ta kwashe wata biyu karkashin dokar kulle da aka sanya domin dakile cutar coronavirus.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasar ya ce janye dokar zai ba da damar bude masallatai domin gudanar da ibadu daga ranar 31 ga watan Mayu.

Kasar Saudiyya ce ta ke da mafi yawan wadanda suka harbu da cutar a yankin Gulf wanda hakan ya sa ta kakaba dokar kulle a kasar a ranar Idin karamar sallah.

Ma’aikatar cikin gidan ta kuma ce za ta fara sassauta dokar hana fitar ne daga 6 na safe zuwa 3 na yamma daga ranar Alhamis zuwa Asabar.

Daga Lahadi har izuwa 20 ga watan Yuni kumua za ta kara lokacin zuwa 8 na dare kafin daga bisani a janye dokar baki daya a ranar 21 ga watan Yuni.

“Daga ranar Alhamis masarautar za ta shiga sabon tsari (na kokarin dakile annobar) wanda za a cigaba da sassautawa tare da tabbatar ba da tazara” inji Ministan Kiwon Lafiya, Tawfiq Al-Rabiah a ranar Litinin.

Saudiyya ta tabbatar mutum dubu 75 sun kamu da cutar coronavirus ciki har da mutu 400 da suka rasu a kasar.

A watan Maris, kasar ta soke gudanar da aikin Umrah saboda fargabar cutar da ke yaduwa a kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya rawaito cewa mahukunta a kasar ba su bayyana ko za a gudanar da aikin hajji a bana ba, amma sun shawarci maniyyata su jinkirta shirye-shiryensu.

A shekarar da ta gabata dai kusan mahajjata miliyan biyu da dubu dari biyar ne suka gudanar da aikin hajjin.