Kasar Saudiyya ta wajabta karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 a matsayin sharin amince wa maniyyata aikin Hajji sauke farali.
Yayin ba da umarnin, Ministan Lafiya na Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah ya ce ya zama tilas ga maniyyata yi karbi rigakafin na COVID-19, domin kasar ba za ta ba da izinin shigar kasar don aikin Hajji ba, sai dole idan an yi masa rigakafin.
- ’Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Sarkin Birnin Gwari
- Za a yanke hukunci kan haramcin yi wa mata kaciya
- Buhari ya yi raddin kan sauke Babban Sufetan ’Yan sanda
Rabiah ya ce: “Dole ne ku shirya da wuri don tabbatar da karfin da ake bukata don gudanar da cibiyoyin kiwon lafiya a Makkah da wurare masu masu tsarki da Madina, da kuma wuraren da mahajjata za su shiga lokacin aikin Hajjin na 2021.”
Ya kara da cewa: “Dole ne a kafa Kwamitin Yin Allurar Rigakafin kwarkwata ga mahajjata da masu Umrah.
“Dole ne a yi rigakafin COVID-19 ga masu son shigowa domin aiki saboda hakan na daga cikin sharuddan aikin Hajjin mai zuwa,” a cewarsa.