Tun bayan tsanantar cutar COVID-19, kasar Saudiyya ta rufe wuraren taruwar mutane ciki har da wuraren shan shisha a kasar.
Sai dai, a wannan karon gwamnatin kasar ta amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a fadin kasar, daga ranar Litinin mai zuwa, bayan da aka sassauta dokar COVID-19.
- Kurunkus: Sunusi II ya zama Halifan Tijjaniyya a Najeriya
- Tsohon Shugaban Kasa IBB tsohon saurayina ne —Ummi Zee-zee
- Kafar Sadarwar Media Trust Za Ta Fara Shirin Podcast Da Hausa
- Dalilin da ma’aikatan asibiti ke wulakanta majinyata
Ma’aikatar kula da birane da karkara ta amince a sayar da shisha ga wadanda aka yi wa rigakafin cutar, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar, SPA, ya ruwaito.
Yayain da za a rika shan shishar a sarari a wuraren shan gahawa, an haramta sha a wuraren cin abinci.
Tun asali, Saudiyya ta rufe gidajen cin abinci da shan gahawa; wadanda yawanci a nan ake shan shisha, a wani mataki na rage tasirin cutar.