✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya ta musanta shirin dakatar da Umara a yanzu

An yi kira ga mahajjata da su ci gaba da bin dokokin yaki da cutar sau da kafa.

Gwamnatin Saudiyya ta musanta jita-jitar cewa tana shirin dakatar da ayyukan Umara saboda yadda annobar cutar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa.

Wata majiya a Ma’aikatar Aikin Hajji ta Saudiyya ta shaida wa shafin Haramain Sharifain cewa babu shirin yin hakan ya zuwa yanzu.

Sai dai kamar yadda BBC ya ruwaito, Ma’aikatar ta yi kira ga mahajjata da su ci gaba da bin dokokin yaki da cutar sau da kafa.

A kwanakin baya hukumomin Masallatan Harami biyu suka dawo da dokar ba da tazara a masallatan biyu bayan karuwar da aka rika samu wajen yaduwar nau’in Coronavirus na Omicron.

A shekarar 2020 ce Gwamnatin Saudiyya ta hana baki zuwa kasar don gudanar da aikin Hajji da Umara, sannan aka takaita adadin masu gudanar da ibadar ta shekara-shekara sakamakon annobar.