Hukumomin kasar Saudiyya na shirin janye batun yawan shekaru da suka kayyade wa masu zuwa kasar domin yin ibadar Umrah daga kasashen ketare.
A baya Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bullo da wani tsari da ya hana duk wani dan kasar waje da ya haura shekara 50 a duniya samun izinin gudanar da ibadar Umrah.
- Saudiyya ta dakatar da ’yan Najeriya shiga kasarta saboda Omicron
- Hotunan bikin bajekolin fina-finai a Saudiyya
Amma a karkashin sabon tsarin, kowane dan kasar waje na da damar zuwa Saudiyya domin yin Umrah, muddin ya haura shekara 18 da haihuwa.
Hakan na kunshe ne a sanarwar da shafin bayar da izinin shiga kasar Saudiyya ta intanet ya fitar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumoin Saudiyya suka ayyana dokar hana shigar baki daga wasu kasashe, bayan bullar kwayar cutar Omicro, wanda nau’i ne na cutar COVID-19.
Miliyoin Musulmai daga sassan duniya ne ke ziyartar Saudiyya a duk shekara domin gudanar da ibadar Umrah da ziyara.
Sai dai bullar cutar COVID-19 ta sa an tataika yawan masu zuwa domin gudanar da ibadar, kafin daga baya a sassauta dokar bayan an samu raguwar alkluman masu kawamu da ita.
Ana kuma fata da wannan sabuwar dokar za a samu karin masu zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da ibadar ta Umrah.