Kasar Saudiyya ta rufe gidajen abinci da wuraren shakatawa a wani sabon mataki na rage taruwar jama’a don taikata yaduwar cutar coronavirus a kasar.
Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta sanar da haramta da bukukuwan daurin aure da sauran taruka a otal-otal da sauran wurare na tsawon kwana 30 daga ranar Alhamis.
- ’Yar aiki ta rataye kanta a Kano
- Matakan soyayya da bayaninsu dalla-dalla
- Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar kan ‘batanci ga Sahabbai’
Gwamantin kasar wadda masu cutar ke ta karawa ta ce gidajen abinci, wuraren shakatawa, wuraren motsa jiki, da gidajen kallo kuma za a rufe su ne na tsawon kwana 10.
Bisa sabuwar dokar, harkokin gidajen abinci za su takaita ne ga sayar da abincin da za a tafi da shi a ci.
Hakan na zuwa ne kwana biyu bayan gwamnatin Saudiyya ta daktar da baiki daga kasashe 20 shiga kasarta.
Kasashen su ne: Amurka, Birtaniya, Jamus, Faransa, Turkiyya, Switzerland, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Afirka ta Kudu da sauransu.
Sai dai ta ce baki ’ya asalin Saudiyya, jakadu, da jami’an lafiya daga kasashen da dakatarwar ta shafa za su samu izinin shiga kasar.
Akalla mutum 368,500 ne suka kamu da cutar coroanvirus a kasar inda ta yi ajalin 6,386 daga cikinsu.
A watan Disamba, kasar mai yawan al’umma miliyan 34 ta fara yi wa ’yan kasarta allurar rigakafin cutar coronavirus, kuma kawo yanzu ta yi wa akalla mutum 391,000.