Masarautar Saudiyya ta dakatar da matafiya daga Najeriya shiga kasarta, sakamakon bullar sabon samfurin cutar COVID-19 na Omicron a Najeriyar.
Sanarwar da aka fitar a ranar Laraba ta ce daga ranar Alhamis za a baki daga ’yan Najeriya shiga Saudiyya, wadda Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Samanta (GACA), ta dakatar da jigilar fasinjojin Najeriya zuwa kasar.
- An sake shirya wa Malamai jarabawar gwaji a Kaduna
- Nan da awa 48 za mu sake tsunduma yajin aiki —ASUU
Wani jami’i a Ofishin Jakadancin Saudiyya a Najeriya a Kano wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce umarnin wani yunkuri ne na dakile shiga Saudiyya da cutar daga Najeriya.
Kazalika wani ma’aikaci a filin tashin jirage da ke Kano ya ce tuni aka bayar da sanarwar dakatar da tashin jiragen masu zuwa aikin Umrah a Saudiyya.
“Har an fitar da sanarwar dakatar da zuwa aikin Umrah, babu wani jirgi da zai tashi daga Najeriya zuwa Saudiyya har sai nan da wani lokaci.
“Ina tunanin sun bi sahun Birtaniya ne wajen zartar da wannan hukunci, saboda hana cutar shiga kasarsu,” kamar yadda ma’akacin ya shaida wa wakilinmu.
Kawo yanzu dai mutum biyar ne aka tabbatar sun harbu da samfurin cutar COVID-19 na Omicron a Najeriya.
A sanarwarta dakatar da jigilar matafiya daga Najeriya zuwa Saudiyya, hukumar sufurin jiragen sama ta Saudiyya, ta ce dokar ba ta shafi ’yan Najeriya da suka shafe mako biyu a wata kasa kafin shigarsu Saudiyya ba.
Sai dai ta ce, “Za a killace ’yan kasa da suka je kasar da aka bayyana na kwanaki biyar, tare da yi musu gwaje-gwaje da kuma rigakafin cutar.”
Aminiya ta rawaito cewa tun bayan dage dokar hana baki shiga Saudiyya saboda bullar annobar COVID-19, mutane da dama suke ta tururuwar zuwa yin ibadar Umrah.