An ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya wanda ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadana.
Shafin Haramain na mahukuntan da ke kula da Masallatan Harami na Makkah da Madinah ne ya tabbatar da hakan.
Saboda haka, gobe Lahadi take Sallah ƙarama a ƙasa mai tsarki.