✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kantoman Ribas ya dakatar da hadiman Fubara

Ya ce umarnin zai fara aiki nan take.

Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.

Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakatare na Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da masu ba da shawara na musamman.

Ya umarci duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukansu ga sakatarorin ma’aikatunsu.

Ya ce hukumomin da babu sakatare, sai a bai wa babban darakta mafi girma ko shugaban gudanarwa.

Wannan umarni ya fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025.