Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta ce yanzu mata ’yan kasa da shekara 45 za su iya zuwa aikin Umarah ba tare da muharrami ba.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, kamar yadda kafar Haramain Sharifain ya wallafa a dandalinta na Facebook a ranar Alhamis.
- Najeriya ce ta 3 a kasashen da suka fi cin naman kare a duniya —Bincike
- Ramadan: An ga watan azumi a Saudiyya
Sanarwar ta ce yanzu mata za su iya zuwa aikin Umarah ba tare da wani muharrami ko kuma wata kungiya ba.
Har ila yau, Saudiyya ta ce yanzu mata ba sai sun kasance cikin wata tawaga ta ’yan uwansu mata ba domin zuwa ibadar ta Umrah.
Sai dai tun bayan fitar sanarwar mutane suka shiga tofa albarkacin bakinsu, ganin cewa sabon mataki da hukumar ta fitar ya ci karo da tsarin addinin Musulunci, kuma tamkar zagon kasa ne ga dokokin addinin.
Dama a baya, hukumar ta bai wa mata damar yin Umarah ba tare da muharrami mai shekara kasa da 40 ba, bisa sharadin cewa dole ne su kasance cikin wata tawaga ta mata.