A daidai lokacin da mahukunta a kasar Saudiyya ke ci gaba da sassauta matakan kare yaduwar COVID-19 an sami sabbin masu dauke da cutar 3,379 yayin da wasu 37 suka rasu a rana guda.
Ma’aikatar lafiyar kasar ta ce mutum 2,213 ne suka warke daga cutar a ranar Lahadi 21 ga watan Yuni, lamarin da ya sanya adadin wadanda suka warke daga cutar ya kai 101,130, wasu 1,267 kuma suka rasu.
A ranar Lahadin ne gwamnatin Saudiyya ta bude masallatai sama da 1,500 da ke fadin birnin Makkah a domin ba wa masallata izinin yin ibada a cikinsu, bayan an yi masu fishin magani.
Gwamnatin ta kuma janye dokar hana fitar dare tare da dawo da daukacin al’amuran cinikayya da harkokin yauda gobe a kasar, amma banda shige da fice zuwa kasashen ketare.
- Saudiyya na duba yiwuwar dakatar da aikin Hajjin bana
- Za a bude masallatai a Saudiyya
- COVID-19: Babban Mufti na Saudiyya ya ce a yi sallar Idi a gida
Ma’aikatar kiwon lafiyar ta shaida cewa akwai mutukar mahimmanci a koma ga al’amuran yau da kullum yadda aka saba a baya sai dai ta nuna mahimmancin bin sabbin ka’idojin kariyar cutar coronavirus wadanda suka hadar da ba da tazara.
Bugu da kari ma’aikatar ta ayyana ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni a matsayin ranar da za a kara sassauta matakan kariyar a karo na uku, inda tayi gargadi cewa annobar na nan bata gushe ba.
Wannan matakin na zuwa ne kafin lokacin aikin Hajji da ke zuwa a karshen matan Yuli, kuma zuwa yanzu mahukuntan kasar ba su kai ga yanke hukuncin ko za a yi aikin Hajji bana ba ko a’a.
Garin Makkah shi ne matattarar Alhazzai amma wani rahoto da kamfanin dillancin labaru na AFP ya ruwaito ya cewa duk da kwararan matakan kariyar cutar da mahukantan kasar ke dauka musamman a Birnin Makkah ana ci gaba da samun yawaitar yaduwar cutar a kasar.
Gwamnatin kasar ta bude masallatan da ke wajen Birnin Makkah ne tun a watan Mayu inda ake yin sallah a bisa ka’idar ba da tazara.