✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sati 6 da barin gidan yari, ya sake shiga hannu kan satar babur

Mutumin ya jima yana sace-sace a Kano, Bauchi da kuma Gombe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta cafke wani mutum kan zargin satar babur, sati shida bayan fitarsa daga gidan gyaran hali.

Mutumin, dan asalin garin Dayi da ke Jihar Katsina, an cafke shi ne a kan titin France Road a Karamar Hukumar Fagge, lokacin da ya yi yunkurin satar wani babur kirar Suzuki.

Kakakin ’yan sandan Jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cafke mutumin.

Shi ma da ya ke karin haske, wanda ake zargin, ya ce satinsa shida kenan da barin gidan yari, bayan kammala wa’adin zaman shekara biyu da aka yanke masa.

“Ni tsohon direban mota ne, tun bayan hatsari da na yi da motata ban samu motar da zan rika neman abinci da ita ba, hakan ne ya sa na shiga sace-sace. Na jima ina sata a Jihohin Kano, Bauchi da Gombe, kuma na saci babura akalla guda 10.

“Lokaci na karshe da aka kama ni shekara biyu aka yanke min, yanzu sati na shida da fitowa. Na rantse da Allah sharrin shaidan ne,” inji shi.

Mutumin mai shekara 56 a duniya, ya ce matansa sun rabu da shi saboda dan hali da ya ke yi, amma ya yi alkawarin wannan shi ne karonsa na karshe da zai sake aikata sata.

“Matana sun guje ni, sun ce ba za su iya zama da barawo ba,” inji shi.

Kazalika, Kakakin ’yan sanda na Kano ya ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Sama’ila Dikko ya ba da umarnin gudanar da bincike na tsanaki akan wanda ake zargin, kafin mika shi zuwa ga kotu.