Wata kotun Musulinci a Kano ta tsare wani matashi mai shekaru 30 a gidan kaso bisa tuhumar sa da satar shadda yadi uku.
’Yan sanda ne dai suka gurfanar mutumin wanda ke zaune a unguwar Tudun Murtala a gaban kotun bisa zargin sa da kuruciyar bera da kuma shiga wuri ba da izini ba.
- Dan haya ya make maigida har lahira kan kudin haya a Abuja
- Masari ya raba tallafi ga mutanen da harin ’yan bindiga ya shafa a Safana
Tun da fari dai, dan sanda mai gabatar da kara, Abdul Wada ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuli a unguwar Danbare da ke jihar, da misalin karfe 10:30 na dare.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya balle shagon wani mai suna Abdulkadir Ibrahim, ya saci wani buhun Leda da yadin ke ciki.
Laifin dai ya saba wa sashi na 133 da na 201 na kundin Dokar Kotin Shari’ar Musulinci.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Alhaji Isma’il Muhammad, ya dage zaman kotun zuwa ranar 3 ga watan Agusta, domin ci gaba da sauraron karar.