An gurfanar da wani maigadi a kotu kan zargin satar bulo 240 a yankin Abuja.
A ranar Litinin ’yan sanda suka maka mai gadin a kotun da ke yankin Kado inda ake tuhumarsa da laifin hadin baki da sata.
- Wata Sabuwa: Dabdalar da ta wakana a Kannywood a makon jiya
- DSS ta cika hannu da ma’aikatan bankin da ke cuwa-cuwar sabbin kudade
Lauyan mai gabatar da kara, Stanley Nwafoaku, ya fada wa kotun cewa a ranar 7 ga Janairu suka mika korafin satar a ofishin ‘yan sanda da ke Life Camp.
Ya ce ya dauki mai kare kansa aiki don tsare masa kamfanin buga bulo dinsa.
Ya yi zargin mai gadin ya hada baki wani wajen sace masa bulo har guda 240 wanda kudinsu ya kai N15, 000.
Laifin da lauyan ya ce ya saba wa sassa na 79 da 289 na dokar ‘Penal Code’.
Shi kuwa lauyan wanda ake zargi, Charity Nwosu, nema ya yi kotun ta ba da belin wanda yake karewa.
Alkalin kotun, Muhammed Wakili, ya ba da belin wanda ake zargi kan N200,000 da shaida daya, kana ya dage shari’ar zuwa 1 ga Maris.
(NAN)