Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a PRP Gama a Jihar Kano ta bayar da umarnin tsare wani matashi a gidan gyaran hali bisa zargin sa sata a wata kotun.
Mai gabatar da kara, Aliyul Abidin, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya balle kofar Kotun Shariar Musulunci da ke Sabon Gari wacce aka fi sani da Kotun Bola inda ya dauke wasu karafuna da kimarsu ta kai Naira dubu 70 da kuma wani inji da kimarsa ta kai Naira dubu 30 da kuma wasu karafunan rodi da kimarsu ta kai Naira dubu 118,000.
Aliyul Abidin ya shaida wa kotun cewa a kan hakan ne aka caji matashin da laifin shiga da aikata laifi da yin sata, wadanda suka saba da sashe na 212 da na 215 da kuma na 133 a Kundin Laifuka na Penal Kod.
Wanda ake zargin ya amsa laifin daukar inji amma ya musanta na daukar karafuna da rodi.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Nura Yusuf Ahmad ya dage shariar zuwa ranar 20 ga watan Satumba, 2022 don yanke masa hukunci tare da ba shi rantsuwa a kan sauran tuhume-tuhumen da ya musanta.
Har ila yau, alkalin ya aike da shi gidan gyaran hali zuwa ranar ci gaba da shari’ar.