✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Qatar na shirin sayen Manchester United

Hukuncin UEFA zai haifar masa da cikas wajen cim ma muradinsa

Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani, ya nuna sha’awarsa ta sayen kunyar kwallon kafa ta Manchester United.

Sai dai mai yiwuwa basaraken ba zai samu cikar burinsa ba har sai Kungiyar Kwallon Kafa ya Nahiyar Turai (UEFA) ta yi wa wata dokarta kwaskwariama da zai ba shi damar haka.

A baya dai, UEFA ta yanke hukuncin cewa bai halasta kungiyoyin kwallon kwafa biyu mallakar mutum guda su shiga gasa daya ba.

Wanda hakan ke nufin United ba za ta samu karawa da PSG ba saboda PSG mallakar Sarkin ce.

Bayyanar labarin burin Sarkin na Qatar ya sa gwiwar da dama daga wadanda suka nuna sha’warsu ta sayen kungiyar, ta yi sanyi.

An dai yi amannar daga cikin masu zawarcin kungiyar, kaf babu wanda tayinsa zai kama kafar na basaraken.

Bayanai sun ce Sarki Hamad al-Thani zai fuskanci cikas dangane da wannan buri nasa muddin ba a yi wa hukuncin da UEFA ta yanke kwaskwarima ba.