Mai Martaba Sarkin Fadan Ninzo da ke karamar hukumar Sanga da ke jihar Kaduna Alhaji Umar Musa yayi kira ga jama’ar masarautrsa da su ci gaba da rungumar zaman lafiya domin shine kadai hanyar samun ci gaba.
Sarkin, yayi wannan kira ne yayin rangadin da ya gudanar a masarautar tasa bayan cika shekara guda hawansa kan karagar masarautar.
Alhaji Umar yace yana gewayawa ne don sanin irin kalubalen da jama’arsa ke fuskanta domin Isar da su ga hukumomin da su ka dace don neman mafita.
Yayinda su ke bayyana ra’ayinsu, Hakimin Fadan Ninzo, Mallam Ibrahim Mamman da Wakilin Fulanin masarautar, Mallam Muhammad Jibril sun yi kira ga mutanensu da su ci gaba da baiwa sarkin gudummawar da ta kamata, sannan su ka bayyana irin matsalolin da al’ummarsu ke fuskanta na rashin tsaftataccen ruwan sha da dakunan shan magani a wasu kauyukan da kuma rashin fitar da labin shanu.
Idan za a iya tunawa jaridar Aminiya ta kawo labarin hawansa kan sarautar a watan Maris na shekarar sa ta gabata inda gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya ba shi sanda.