Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kaurace wa jana’izar diyar Sardaunan Sakkwato, Aisha Ahmadu Bello, wadda aka gudanar a masallacin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello a yau Alhamis.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutane sun cika da mamakin rashin ganin Sarkin Musulmi a wurin jana’izar ganin tun sanda aka bayar da labarin rasuwarta a ranar Jumu’a da ta gabata, yana cikin jihar Sakkwato.
Sai dai kuma gabanin isowar gawarta aka samu labarin cewa Sarkin ya bar garin domin wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Wasu na zargin rashin halartar Sarkin musulmi na da nasaba ne da tsamin dangartakar da ke tsakaninsa da magajin garin duk dai ba a tabbatar da hakan ba.
Jami’in hulda da jama’a na majalisar Sarkin musulmi, Aminu Haliru Gidadawa, ya ce ba shi da ta cewa game da lamarin don ba shi ya kamata a tunkara da maganar ba.
An binne gawar Aisha Ahmadu Bello ce a makabarta Magajin Garin Sakkwato da ke unguwar Binanchi kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Hajiya Aisha Ahmadu Bello ta rasu tana da shekara 76, a wani asibiti a birnin Dubai da ke Haddaddiyar Daular Larabawa, bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda danta, Hassan Dambaba, ya sanar.
Marigayiyar, wadda aka fi sani da suna Hajiya A’i ita ce ta biyu a cikin ’ya’yan marigayi Sardauna, kuma mata ce ga marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmad Danbaba.
Marigayiyar ta bar jikoki 26 da ’ya’ya biyar ciki har da Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba da Asma’u, matar Sarkin Sudan, Shehu Malami.
Daga cikin dimbin jama’ar da suka halarci jana’izar akwai Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan da jagoran majalisa, Sanata Yahaya Abdullahi da Sanata Aliyu Wamakko, Sanata Danjuma Goje da Sanata Abdullahi Ibrahim Gobir.
Sauran sun hada da Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Yobe Mai Mala Buni da na Kano Abdullahi Ganduje da tsohon gwaman Zamfara, Abdul’aziz Yari da Aliko Dangote da Dahiru Mangal da kuma Janar Aliyu Gusau da sauransu.