Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya.
Sarkin Musulmi ya buƙaci al’ummar Musulmin Najeriya da su tashi da azumi a ranar Asabar, 1 ga watan Maris 2025, zuwa ƙarshen watan, mai kwanaki 29 zuwa 30.
Da yake sanar da ganin watan a fadarsa da ke Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya bayyana cewa an tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a garuruwan Bama da Maiduguri da ke Jihar Borno da ma wasu wurare.
Don haka, Asabar 1 ga watan Ramadan 1446 Bayan Hijira, ta yi daidai da 1 ga watan Maris 2025 Miladiyya.
- An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya
- Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Nabamamu a Zamfara
Sanarwar tasa ta zo ne ’ sa’o’i bayan hukumomin ƙasar Saudiyya sun tabbatar da ganin watan a Ƙasa Mai Tsarki.
Sarkin Musulmi ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.
Ya roki mutane su yi wa kasa da shugabanni a addu’a domin samun ɗorewar zaman lafiyaa Najeriya.