✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fara duban watan Shawwal – Sarkin Musulmi

Idan an ga watan, hakan na nufin za a yi sallah ƙarama a ranar Lahadi.

Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammad Sa’ad Abubakar, ya umarci al’umma da su fara duban watan Shawwal daga gobe Asabar, 29 ga watan Ramadan 1446, wanda ya yi daidai da 29 ga watan Maris, 2025.

Shugaban kwamitin harkokin addini na masarautar Sakkwato, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce duk wanda ya ga jinjirin watan Shawwal ya sanar da Hakimi ko Uban Ƙasa mafi kusa da shi, domin a kai rahoto ga Sarkin Musulmi.

Wazirin Sakkwato, ya yi addu’a Allah Ya taimaka musu a wannan muhimmin aikin na addini da suke yi.

Idan aka dace da ganin watan Shawwala a ranar Asabar, hakan na nufin za a yi sallah ƙarama a ranar Lahadi, akasin haka kuma za a yi sallah a ranar Litinin.

Yanzu haka dai al’ummar Musulmi sun mayar da hankali wajen shirye-shiryen bikin sallah ƙarama na bana.