Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya musanta cewa akwai tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamnatin Sakkwato.
Ana iya tuna cewa bayan karɓar akalar jagoranci ne Gwamna Ahmed Aliyu ya yi wa Dokar Masarautar Sakkwato gyaran fuska tare da sauke wasu sarakunan gargajiya, lamarin da aka riƙa raɗe-raɗin wani yunƙuri ne tsige shi kansa Sarkin Musulmin.
Sai dai da yake jawabi a saƙonsa na barka da sallah, Sarkin Musulmi ya ce “ba wata rashin jituwa ko faɗa a tsakaninmu.
“Muna aiki tare a koyaushe. Aikinmu mu taimaka wa gwamnatin [Sakkwato] kan shirye-shiryen da ta ɗauko domin ciyar da jama’a gaba.”
Ya yi kira ga al’ummar musulmi da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a domin samun nasara wajen sauke nauyin jama’a da rataya a wuyansu.
Kazalika, Alhaji Sa’ad ya ce karantarwar addini da aka samu a watan Azumi mai albarka abu ne da ya kamata a riƙe a sanya cikin aiki.
“Mu ƙara ɗaure ɗamara kar mu koma gidan jiya wajen aikata saɓon Allah. Mu dage da yin ibada kar a ja baya. Sannan mu riƙa yi wa shugabanni addu’a.
“Ku kuma shugabanni ku ji tsoron Allah cikin jagoranci. Idan za a yi ayyukan jama’a kar a ji tsoron kowa sai Allah,” in ji Sarkin Musulmi.
Sarkin ya yi kira ga jami’an tsaro da su ktara ƙaimi wajen magance matsalar tsaro domin a cewarsa har yanzu akwai sauran aiki a ba iya Jigar Sakkwato kaɗai ba.