✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Jama’are Ahmadu Muhammad Wabi III ya rasu

A watan Nuwambar 2020 ya cika shekara 50 a kan karagar mulki.

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jama’are Alhaji Dokta Ahmadu Muhammad Wabi III rasuwa.

Ya rasu ne da misalin karfe 12 na daren Asabar, wayewar garin Lahadi kamar yadda Gado Da Masun Jama’are, Alhaji Saleh Malle ya tabbatar wa BBC.

Sarkin dai ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Ahmadu Muhammad Wabi III ya bar mata biyu da ’ya’ya 35 da kuma jikoki da dama.

A watan Nuwambar 2020 ya cika shekara 50 a kan karagar mulki.

Ana sa ran yin jana’izarsa idan anjima a garin na Jama’are.