Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II (CON) ya yi kira ga daukacin jama’ar masarautarsa da su kasance tsintsiya madaurinki daya don kara samun zaman lafiya da ‘yan uwantaka ba tare da nuna bambanci ba kamar yadda aka shaidi masarautar da yin hakan tun da dadewa.
Sarkin yayi wannan kiran ne a wajen Walimar shan Ruwa da ya shirya a Fadarsa da ke Garin Kafanchan a karshen Makon da ya gabata.
Sarkin, wanda ya nuna matukar jin dadinsa ga wadanda suka amsa gayyatarsa, yace manufar shirya wannan walimar ita ce nuna godiya ga Allah game da albarkar Watan Ramadan da ya azurta Musulmai da shi tare da kuma nunawa duniya irin zaman lafiyar da ya samu a yankinsa da kuma yadda ya ke zaman lafiya tare da rungumar kowa a masarautarsa.
Da ya ke jawabi a madadin Kiristocin Karamar Hukumar Jama’a, Sakataren yada Labarai na Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen Karamar Hukumar Jama’a Rabaran Musa Ishaku, ya nuna jin dadinsa da gayyatar da Sarkin yayi musu inda yace Kungiyarsu ta CAN na bada cikakken goyon baya ga Masarautar kuma a shirye su ke a duk lokacin da ake bukatar gudummawarsu kowace iri ce don habaka zaman lafiya da ci gaban Masarautar.
Rabaran Ishaku ya kara da cewa an umurce su a cikin littafin Baibul da su zamo masu biyayya da kuma yin addu’a ga Shugabanninsu a kan haka yace, Kungiyarsu, na tare da Masarautar kan duk wani kuduri na ci gaba da za ta fito da shi don samun karin hadin kai a tsakanin Mabiya Addini da ke Masarautar.
Tunda farko, Shugaban Karamar Hukumar Jama’a Peter Danjuma Aberik wanda Sakataren Karamar Hukumar, Amos Sama’ila ya wakilta ya yabawa Sarkin kan shirya irin wannan walima da ya tattaro Jama’ar Masarautar Musulmai da Kiristoci su ka zauna waje daya don kara kulla zumunci a tsakaninsu.
Ya kuma bayyana Sarkin a matsayin mai abin koyi wajen son zaman lafiya da kuma nuna kyakkyawan Shugabanci ba tare da la’akari da kabilar Mutum ko Addininsa ba.
Sama’ila, wanda ya yi kyakkyawan addu’a ga Sarkin kan karin lafiya da tsawon rai da hikima da juriyar Shugabanci ya kuma koka kan yadda Karamar Hukumar Jama’a ke samun nakasu a kudaden da ya ke zuwa mata daga Gwamnatin Jiha tare da wasu kananan hukumomi takwas da ke jihar Kaduna inda ake yanke musu kudaden a matsayin horarwa daga Gwamnatin jiha kan rashin zaman lafiya, abinda yace dalilin da ya sa Shugabannin Kananan Hukumomin su ka tuntubi Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa’i kan ya sassauta musu don su rika samun kudaden aiwatar da ayyukansu da ke gabansu maimakon zaftare musu da ake yi ana baiwa harkar tsaro rabi yayinda su kuma ake basu ragowar rabin.
Daga nan yayi kira ga jama’ar Karamar Hukumar da su guji duk wani nau’i na tashin hankali tare da hada kansu don samun damar yi musu aikin da zai cicciba Karamar Hukumar zuwa mataki na gaba.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugabannin Sojoji da na ‘yan Sanda da na Cibil Defence da DSS da Bijilenti da Shugabannin bankunan da ke garin da Wakilin Kungiyoyin Addinin Musulunci da na Kirista da kuma masu dauke da rawunnan Gargajiya na Garin da wadanda suka zo daga garuruwan Kaduna da Abuja.