✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki ya nuna takaicinsa kan yadda nazarin adabi da karance-karance suka yi kasa warwas

Sarkin Suleja da ke Jihar Neja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, ya nuna takaicinsa kan yadda dakunan karatu da ke alkinta dimbin litattafan adabi da sauran…

Sarkin Suleja da ke Jihar Neja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim, ya nuna takaicinsa kan yadda dakunan karatu da ke alkinta dimbin litattafan adabi da sauran kayan karatu da ke bunkasa tunanin matasan kasar nan suka gushe

Ya ce dakunan karatu na zamani, wanda aka fi sani dakunan karatun na’urar kwamfuta ko na zamani, wato “E-Books” sun karya lagon al’adar karatun littattafai a tsakanin matasa, wadanda a halin yanzu suke sarayar da lokacinsu wajen bibiyar shafukan intanet da tattaunawa a shafukan sada zumunta.

Sarkin ya fadi hakan ne Litinin din nan a babban taron duniya kan adabin Arewacin Najeriya karo na 11, da aka gudanar a hedkwatar Budaddiyar Jami’ar kasa ta Najeriya (NOUN) da ke Abuja.

Taron na kwana biyu, mai taken “adabi da ci gaban zamani a Arewacin Najeriya,” ya tattaro mahalarta daga daukacin fadin tarayyar kasar nan da kuma kasashen waje. Ana sa ran sun tattauna kan yadda ake tarairayar adabi da kimar matakin da ya kai a yankin.”

Sarkin da yake karin haske kan daklin karatun zamani na E-Library, cewa ya yi, a zamaninsu cikin shekarun 1950 sukan karanta dimbin littattafai wadanda suka hada da tarihi da al’adun al’ummomi, wadanda ke kara zaburar da su da kaimin neman ilimi.

Ya shawarci mahalarta taron da su tattauna kan yadda za abunkasa karance-karance a tsakanin matasan Najeriya matukar kasar nan na son ta sake samar da hamshakan masanan marubutan adabi irin su Wole Soyinka da chinua Achebe da Zaynab Alkali da sauransu.

Shi kuwa babban bako mai jawabi, Farfesa Graham Furniss na Jami’ar Landan, cewa ya yi makalarsa ta mayar da hankali kacokam ne kan al’amuran da suka shafi “bambancinmu da hadin kanmu.” 

Furniss wanda ya dauki tsawon lokaci yana bayani kan “bibiyar bambance-bambance da nauyin da ya rataya na ilimi da nazarin al’adu sannan ya yi godiya ga wadanda suka shirya taron saboda gayyatarsa da suka yi don halartar wannan taro da ke da kaimin alkinta adabi a Arewacin Najeriya.

A matsayinsa na wanda ya shafe shekara 40 yana nazarin adabin Hausa da al’adu, Furniss ya yi nuni da cewa babban kalubalen da ke fuskantar cibiyoyin ilimi wajen nazarin Hausa shi ne rashin tattara bayanai da alkintasu.

“Aikin kwatanta kima da nazari da adanawa da yadawa su ne manyan matsalolin da suka haifar da ganin barazanar da ke tunkarar Hausa, ha rake bukatar kariya, ko kuma in an yi wa Hausa kallon wani fannin da ke bijiro da al’amura, inda suke da managartan furanni da za su yi ta girma, masu rauni kiwa su karairaye su fadi kasa.

“Ko ta wace fuska  aka kalli lamarin, akwai dimbin al’amuran da ya kamata a yi nazarinsu, sannan a adana su don al’umma masu tasowa nan gaba,” a cewar Furniss, wanda ya fito daga cibiyar nazarin al’adun Asiya da Afirka da ke Jami’ar Landan.

Ya ce duk da cewa koyar da Hausa a Cibiyar nazarin Al’adun asiya da Afirka ya yi kasa warwas, kimar da aka bai wa harshen wajen nazari a Najeriya na da matukar karfafa gwiwa, tare da fatan cewa makarantarsa za ta ci gaba da hadin gwiwa da cibiyoyin ilimi na Najeriya a fannonin bincike da koyarwa.

Shugaban kwmaitin shirya taron, kuma shugaban Tsangayar fasaha na jami’ar NOUN, Farfesa Godwin Akper, ya bayyana wa mahalarta taron cewa al’amuran da ke faruwa a yankin su suka taimaka wa masana wajen fito da dabarun shawo kan matsaloli.