✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Sanusi II ya soma zaman fada a Kano

Wasu kwamishinoni da muƙarraban gwamnatin Kano na daga cikin mutanen da ke kai gaisuwa.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya soma zaman fada karon farko bayan mayar da shi karagar mulki da Gwamnatin Kano ta yi.

Bayanai sun ce Sarkin ya fito daga gidan sarki a kan doki inda ya zarce fada domin fara zaman fadanci.

Magoya bayan sarkin da dama ne suka taru a lokacin da ya fito, inda suke miƙa caffa da gaisuwa ga sarkin.

Da shigarsa, Sarkin Muhammadu Sanusi II ya hau kan karagar mulki, inda hakimai suka riƙa kai gaisuwa tare da mubaya’a ga sabon sarkin.

Wasu kwamishinoni da muƙarraban gwamnatin Kano na daga cikin mutanen da ke kai gaisuwa ga sabon sarkin a fadarsa.