Kungiyar Mata Musulmi ta Kasa FOMWAN reshen Jihar Gombe ta bayyana cewa sanya Hijabi ga mata ba abun ba ne face hakan ma wani rukuni na tabbatar da cikar addinin ’ya mace.
Shugabar kungiyar, Hajiya Amina Suleiman ce ta bayyana hakan a lokacin bikin zagayowar Ranar Hijabi ta Duniya na shekarar 2022.
- Guguwar Batsirai ta hallaka gommai a Madagascar
- Wadanda ake zargi da kashe Hanifa sun rasa lauyan da zai tsaya musu a Kotu
A cewarta, sanya Hijabi abun alfahari ne ga mata, lamarin da ta yi kira ga Malaman addinin musulunci da su ci gaba da fadakar da mabiya muhimmancin sanya hijabi ga Mata a lokutan wa’azuzzuka da lokutan hudubobin da suke gabatarwa a sallar Juma’a.
Da yake gabatar da kasida a wajen bikin zagoyawar ranar hijabi mai taken ‘Hijabi Mayafinmu ne ba wani abun laifi ba ne’, Malam Musa Muhammad Muhammad, ya ce Allah da kanSa Ya umurci Mata da su sanya hijabi don suturce dukkan sassan jikin su.
Malam Musa Muhammad da ya kasance bako mai jawabi a wurin taron, ya kuma bayyana cewa rashin sanya hijabi da wasu matan kan yi sabawa umurnin Allah ne.
Sannan ya hori mata da su guji sanya hijabi mai sharashara ko wanda zai bayyana surar jikin su.
Da take tsokaci, Malama Zainab Haruna, ta ce sun taru ne don gudanar da bikin Ranar Hijabi ta Duniya saboda su kara fito da muhimmancin sanya hijabi ga ‘yar musulma.
Malama Zainab ta yi kira ga mata da cewa suji tsoron Allah wajen sanya hijabi, tana mai cewa kar su sanya hijabi kuma su rika fakewa da shi suna aikata masha’a.
“Akwai wasu da suke sanya hijabi don samun kariya da batar da kama wajen fakewa su aikata alfasha,” a cewarta.
Ita ma tsohuwar Shugabar FOMWAN reshen Jihar, Malama Fatima Usman, ta bayyana dalilai da kuma tarihin da ya sa aka fara gudanar da bikin Ranar Hijabi ta Duniya tun a shekarar 2013.
“Tun a lokacin da wata mai suna Nasmal Hal ’yar kasar Indiya ta fuskanci cin zarafi har ta kai aka nemi hanata izinin shiga jami’a saboda ta sanya hijabi, a kan haka ne ta jajirce da ta kai ga ta samu goyon baya har aka fara gudanar da bikin ranar a kowacce ranar 1 ga watan Fabarairu kowace shekara.
A jawabinta na godiya Hajiya Bintu Aliyu Summonu, babbar mai taimaka wa uwargidan gwamnan Jihar Gombe Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba wa kungiyar FOMWAN bisa shirya wannan taro da kuma malaman da suka yi fadakarwa kan muhimmancin sanya hijabi ga musulmi.