Sanatocin Arewacin Najeriya sun bukaci shugabannin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS da su janye takunkumin da suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar sanadiyyar juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Ana iya tuna cewa a cikin watan Yuli ne shugabannin ECOWAS suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar takunkumi bayan da sojoji suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
Takunkumin ECOWAS ya hada da dakatar da duk wata huldar kasuwanci da Nijar.
Haka kuma, Najeriya da ke maƙwataka da kasar ta katse wutar lantarki da take bai a yayin da Ivory Coast ta dakatar da shigar da kayayyaki daga kasashen waje zuwa kasar.
Sai dai Sanatocin bayan wani zama da suka yi jiya Talata a zauren Majalisar Dattawa, sun bukaci shugabannin kasashen Yammacin Afirka da su janye takunkuman.
Sun kuma bukaci gwamnatin Nijar da ta saki hambararren shugaban kasar Bazoum tare da fitar da wa’adin mika wa farar hula mulki nan da shekaru biyu.
Sanarwar da Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi) ya karanta, sun ce, “Kungiyar Sanatocin Arewa, ta yi Allah-wadai da dakile tsarin dimokuraɗiyya da sojoji suka yi a wasu yankuna na Yammacin Afirka.
“Zauren ya yi Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar baki daya. Muna rokon gwamnatin mulkin soja a Nijar da su bi bukatun wasu kasashe ta hanyar sakin shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa.
“Kungiyar Sanatocin Arewa ta kuma bukaci gwamnatin mulkin soja a Nijar da ta kawo jadawalin mika mulki wanda ba zai wuce shekara biyu ba.
“Kungiyar Sanatocin Arewa ta bukaci kungiyar ECOWAS da ta dage takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar saboda sha’anin kasuwanci a yankunan iyakokinmu.
“Yana da muhimmanci kada ‘yan Nijar su sha wahala sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasarsu kamar yadda muke ganin abin da ke faruwa a Gaza.
“Muna rokon shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojojin tarayyar Najeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, ya taimaka a mayar da wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar.”