✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 11 a Kebbi

Rahotannin jami'an tsaro sun ce motar ta kwace ta shiga daji da mutanen da ke cikinta.

Akalla mutum 11 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin wata tirela da ya auku a hanyar Maiyama/Koko da ke Jihar Kebbi.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya fitar, ya ce motar na dauke da fasinjoji 65, wadanda dukkaninsu maza ne daga Jihar Sakkwato.

Bayan fasinjojin, tirelar na kuma dauke da buhun albasa da buhun wake da babura shida da ta taso daga Karamar Hukumar Goronyo da ke Sakkwato zuwa Jihar Neja.

“A lokacin da direban motar ya kai kusa da kauyen Dada, a Karamar Hukumar Koko/Besse, birki ya kwace wa direban motar.

“Saboda haka, babbar motar ita kadai ta shiga daji. Sakamakon haka, fasinjoji 65, dukkaninsu maza daga Jihar Sakkwato, ciki har da direban sun samu munanan raunuka.”

Da samun rahoton faruwar hatsarin, Abubakar ya ce an aike da tawagar ‘yan sandan da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa daga sashin Koko zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kai wadanda lamarin ya rutsa da su babban asibitin Koko.

Ya ce yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum 11, sauran wadanda abin ya shafa ana duba lafiyarsu a asibitin.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Chris Omonzokpea Aimionowane, ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu.

Ya kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya, tare da gargadin direbobi da su guji wuce gona da iri da kuma tukin ganagnci.