✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin Kannywood, Suleman Alaqa ya rasu

Jarumin ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Allah Ya yi wa jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Suleman Alaqa rasuwa.

Jarumin ya rasu ne a ranar Litinin, bayan ya sha fama da gajeriyar rashin lafiya.

Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i, Abba El-Mustapha ne, ya sanar da rasuwar jarumin a shafinsa na Instagram.

“Allah Ya yi wa ɗan uwa abokin aiki, jarumi Suleman Alaqa rasuwa yau (Litinin), bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

“Za a yi jana’izarsa a gidansu da ke unguwar Gwammaja da misalin ƙarfe 4 na yamma.

“Muna addu’ar Allah Ya jiƙansa ya gafarta masa kurakuransa ya sa Aljanna ce makomarsa. Idan tamu ta zo Allah Ya sa mu cika da kyau da Imani,” kamar yadda ya wallafa.

El-Mustapha, ya ce za a yi jana’izar jarumin a unguwar Gwammaja da ke birnin Kano da misalin ƙarfe 4 na yamma.

Tuni jarumi a masana’antar suka shiga yi wa marigayin addu’a da neman gafara a wajen Ubangiji.

Idan ba a manta ba Kannywood ta girgiza da mutuwar wasu jiga-jigan jarumanta, kamar Saratu Gidado (Daso) da Darakta Aminu S. Bono, wanda Allah Ya karbi abunsa a baya-bayan nan.