Aƙalla akuyoyi 120 ne aka ruwaito sun mutu, yayin da wata tirela ɗauke da kaya da mutane ta faɗo daga kan gadar titin Zariya a Jihar Kano.
A cewar kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, hukumar ta samu kiran gaggawa daga DPO ɗin ofishin ‘yan sanda na Ƙwalli, SP Muhd Auwal Abubakar da misalin ƙarfe 3:30 na dare.
Ya ce hukumar ta tura jami’anta zuwa wajen da hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 3:42 na dare.
Ya ce “Doguwar tirela mai lamba KMC 311 QZ ɗauke da mutum 90, akuyoyi 199 da babura ƙirar Bajaj guda biyar wadda ta taso daga Mai’adua zuwa Legas ta faɗo daga gadar titin Zariya.
“An ceto mutum 25 cikin mawuyacin hali, an kuma ceto mutum 49 ɗauke da munanan raunuka, sai kuma mutum 17 da aka ceto waɗanda ba su ji rauni ba. Don haka akuyoyi 120 sun mutum an kuma ceto 79 a raye.”
Ya ƙara da cewar hukumomin tsaro a jihar sun kai waɗanda suka ji rauni asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da kuma waɗanda aka ceto cikin mawuyacin hali zuwa asibitin koyarwa na Abdullahi Wase.
Har wa yau, ya ce an miƙa waɗanda hatsarin ya rutsa da su ga jami’in ɗan sanda na ofishin ’Yar Akwa, yayin da aka bayyana musababbin hatsari da gudun wuce ƙima.