✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya kashe mutane 5 a Yobe

Direban bas ɗin ya afka kan mutane da ke tsaye a bakin titi ana tsaka da cin kasuwa.

Aƙalla mutane biyar sun mutu yayin da 19 suka raunata, a dalilin wani hatsarin mota da ya rutsa da su a Kasuwar Damagum da ke kan babbar hanyar Kano-Maidugri a Jihar Yobe.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi.

Wani da lamarin ya faru a idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa, gudun wuce sa’a da wani direban bas ke yi ne ya janyo hatsarin, inda ya afka wa mutanen da ke tsaye a bakin titi ana tsaka da cin kasuwar.

“Direban ya ɗauko fasinjoji ne zuwa Damaturu, kuma da alamu Potiskum ya  nufa,” in ji shi.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen Jihar Yobe, CC Livinus Longzen Yilzoom, ya tabbatar da mutuwar mutane biyar, yayin da 19 kuma suka samu raunuka.

Daga nan ne kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu, da kuma al’ummar Damagum da Jihar Yobe baki ɗaya.